Gwamna Fubara Ya Bayyana Dalili 1 da Yasa Ya Amince da Yin Sulhu a Rikicinsa da Wike

Gwamna Fubara Ya Bayyana Dalili 1 da Yasa Ya Amince da Yin Sulhu a Rikicinsa da Wike

  • Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi magana kan dalilin amincewa da yin sulhu da tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike
  • Fubara ya bayyana cewa ya yarda da sulhun ne domin a samu zaman lafiya a jihar ta yadda za a samu cigaban da ya dace
  • Gwamnan ya yi nuni da cewa ko kaɗan bai ɗauki matakin yin sulhun ba saboda tsoro sai dai kawai domin son al'umma da girmama dattawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta shiga cikin wani ƙazamin yaƙin siyasa da zai kawo cikas ga cigaban jihar ba.

Ya kuma bayyana cewa matakin da gwamnatinsa ta ɗauka a rikicin siyasar jihar ba don tsoro ba ne, sai domin a samu zaman lafiya a jihar, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Ana dab da yanke hukunci Gwamna Abba ya nemi wata muhimmiyar bukata 1 daga attajiran Kano

Gwamna Fubara ya yi magana kan sulhunsa da Wike
Gwamna Fubara ya fadi dalilin yin sulhu da Wike Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ce Fubara ya bayyana haka ne a daren ranar Litinin a lokacin da yake jawabi ga al’ummar jihar Rivers a wajen liyafar sabuwar shekara da gwamnatinsa ta gudanar a gidan gwamnati da ke Port Harcourt.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan, wanda ya yi wa al’ummar jihar fatan alheri da cigaba a shekarar 2024, ya roƙe su da su rungumi shirin zaman lafiya da ake yi a halin yanzu wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta.

Meyasa Fubara ya amince da yin sulhu da Wike?

A kalamansa:

"Duk matakin da muka yanke ba domin tsoro ba ne, amma saboda muna da muradin mutanenmu kuma muna girmama dattawa.
"Ina kira ga dukkan mu da mu rungumi zaman lafiya. Muna buƙatar wannan zaman lafiya domin manufarmu ga jihar ba domin amfanin kanmu bane, sai domin cigaban jihar".

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya kori SSG Abdullahi Baffa Bichi? Gaskiya ta bayyana

Fubara ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar barin tarihin haɗin kai da cigaba a jihar Rivers, ba wai tarihin rikicin siyasa ba.

Gwamna Fubara Ya Yi Magana Kan Yin Murabus

A wani labarin kuma, kuma kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa babu rikicin da zai sanya ya haƙura da muƙaminsa.

Gwamnan ya yi nuni da cewa zai cigaba da jajircewa wajen ganin ya kawo ayyukan da za su amfani mutanen jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel