Kano: Gwamnan Abba Ya Faɗi Gaskiya Kan Tsoma Bakin Shugaɓa Tinubu a Hukuncin Kotun Koli

Kano: Gwamnan Abba Ya Faɗi Gaskiya Kan Tsoma Bakin Shugaɓa Tinubu a Hukuncin Kotun Koli

  • Abba Gida-Gida ya tabbatar da cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bai tsoma baki a shari'ar zaben gwamnan jihar Kano ba
  • Gwamnan ya ce duk da matsin lamba daga wasu tsiraru, Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima ba su shiga lamarin ba
  • Ya buƙaci babban abokin hamayyarsa da magoya bayansa su taho a haɗa kai wajen gina sabuwar Kano

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - A halin yanzun dai kotun kolin Najeriya ta binne duk wata taƙaddama kan zaben gwamnan jihar Kano da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Jaridar Vanguard tace Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da mataimakinsa, Ƙashim Shettima ba su tsoma baki a shari'ar Kano ba.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Gida-Gida ya aika muhimmin sako ga Gawuna bayan hukuncin Kotun Koli

Gwamna Abba, Tinubu da Gawuna.
Kotun koli: Tinubu bai tsoma baki ba duk da matsa masa lamba, Gwamna Abba Hoto: Abba Kabir Yusuf, Bola Ahmed Tinubu, Nasiru Yusuf Gawuna
Asali: Facebook

Abba ya ce duk da matsin lambar da suka sha daga wasu ƴan zuga, Tinubu da Shettima ba su yarda sun yi katsalandan a shari'ar zaben ba har aka karkare ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a harabar kotun koli da ke Abuja jim kadan bayan yanke hukunci jiya Jumu'a.

Idan baku manta ba, mai shari'a Okoro ya soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na tsige gwamnan Kano, kana ya tabbatar da shi a matsayin sahihin wanda ya ci zaɓe.

Wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na gidan gwamnatin Kano, Aliyu Yusuf, ya fitar, ta ce gwamnan ya yi farin ciki da yadda su Tinubu da Shettima ba su taba shiga ƙarar ba.

Sanarwan ta ce:

"Gwamnan ya nuna farin cikin yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima ba su tsoma baki a cikin hukuncin kotun koli ba duk da matsin lamba daga wasu baragurbi."

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya maida martani bayan kotun ƙoli ta yanke hukunci, ya gode wa wanda ya ba shi nasara

Abba ya aika saƙo ga Gawuna da mambobin APC

Gwamnan wanda ke cike da farin ciki ya kuma mika hannun abota ga babban abokin hamayyarsa a inuwar jam'iyyar APC, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna.

Ya buƙaci Gawuna da magoya bayansa na APC su taho su haɗa hannu a gwamnatinsa domin gina jihar Kano zuwa mataki na gaba.

IBB ya yi magana kan mulkin soji a Najeriya

A wani rahoton na daban Ibrahim Badamasi Babangida ya ce ba ya tunanin sojoji zasu ƙara kutse su karɓe ragamar mulkin ƙasar nan.

Tsohon shugaban ƙasa na mulkin sojan ya ce shiga harkokin siyasa da masu kaki suka yi a baya shi ne ya kawo maƙasu ga ci gaban ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel