Shugaba Tinubu Ya Yabawa Gwamnan PDP Bayan Ya Yi Muhimmin Abu 1

Shugaba Tinubu Ya Yabawa Gwamnan PDP Bayan Ya Yi Muhimmin Abu 1

  • Shugaba Bola Tinubu ya yabawa Gwamna Fubara kan yadda ya jajirce domin kawo ƙarshen rikicin jihar Rivers
  • Shugaban na Najeriya ya godewa Fubara bisa shirinsa na aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da ya rattabawa hannu da magabacinsa, Nyesom Wike
  • Fubara yana cikin tawagar ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) da suka ziyarci Tinubu a gidansa na Legas a ranar Talata, 26 ga Disamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar River bisa matakin da ya ɗauka na baya-bayan nan.

Tinubu ya yabawa Gwamna Fubara
Shugaba Tinubu ya yabi Gwamna Fubara kan sasantawa da Wike Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Tinubu ya yabi Fubara yayin da ya amince ya sasanta da Wike

Tinubu ya yabawa Fubara kan abin da ya bayyana a matsayin ƙoƙarin gwamnan jihar wajen warware rikicin siyasar da ke tsakaninsa da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Kotun Koli na shirin yanke hukunci kan zaben Kano, Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin saƙo ga Ganduje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatin tarayya da na jihohi na da alhakin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar nan, inji rahoton jaridar The Punch.

Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar ya fitar ta ruwaito Tinubu a ranar Talata, 26 ga watan Disamba yana cewa:

"Najeriya na bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali domin cigaba. Najeriya ta mu ce, kuma dole ne mu kula da ita."

Wane yabo Tinubu ya yi wa Fubara?

Jaridar Channels tv ta ruwaito cewa, Shugaba Tinubu ya yaba da halartar Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers a wajen taron, inda ya yaba masa bisa ƙoƙarinsa na warware matsalolin siyasar jihar cikin lumana.

Tinubu ya gaya wa Gwamna Fubara cewa:

"Na gode maka kan matsayar ka. Na saurari bayananka da kuma jaddada zaman lafiya. Da zaman lafiya ne kawai za a samu ingantacciyar gwamnati, kuma an fara gudanar da mulki da gaske a ƙarƙashin kulawa ta.”

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Shugaba Tinubu ya tilasta Gwamna Fubara sa hannu kan yarjejeniya? Shugaban PDP ya fadi gaskiya

PDP Ta Ja Kunnen Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi magana kan yarjejeniyar da Gwamna Fubara na jihar Rivers ya amince da ita domin sasantawa da Wike.

Jam'iyyar ta ja kunnen gwamnan da kada ya aiwatar da yarjejeniyar, domin a cewarta hakan ya saɓa doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel