2027: Babban Malamin Addini Ya Yi Magana Kan Yiwuwar Samun Dan Kabilar Igbo a Matsayin Shugaban Kasa

2027: Babban Malamin Addini Ya Yi Magana Kan Yiwuwar Samun Dan Kabilar Igbo a Matsayin Shugaban Kasa

  • Primate Elijah Ayodele ya ce bai ga shugabancin Najeriya zai je hannun ɗan ƙabilar Igbo a zaɓen 2027 ba
  • Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spirit Church, ya bayyana cewa, ko da ƴan kabilar Igbo sun tunkari zaɓen shugaban ƙasa na 2027 da haɗin kai, burinsu zai ƙare a banza
  • Malamin mai fada a ji ya ce za a ɗauki lokaci mai tsawo kafin ƴan ƙabilar Igbo su samar da shugabancin Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Primate Babatunde Elijah Ayodele ya ce ba za a samu shugaban ƙasa ɗan ƙabilar Igbo ba a babban zaɓe mai zuwa na shekarar 2027.

Ayodele, a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba, ya ce ko da dukkanin ƴan ƙabilar Igbo a Najeriya za su haɗu, "ba za a ba su shugabancin ƙasa ba."

Kara karanta wannan

Daga karshe an bayyana dalilin da ya sanya Atiku da Peter Obi suka kasa yin nasara kan Tinubu a kotu

Fasto Ayodele ya ce Igbo ba za su samu shugabancin Najeriya ba
Ayodele ya dusashe fatan yan kabilar Igbo na samun shugabancin Najeriya Hoto: Primate Babatunde Elijah Ayodele
Asali: Facebook

Ba za su ba Igbo shugabancin ƙasa ba" - Ayodele

Gabanin zaɓen shekarar 2027, da alama neman shugaban ƙasa daga shiyyar Kudu maso Gabas, yana jawo damuwa daga masu ruwa da tsaki a faɗin ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan dai ya faru ne yayin da ɗan takarar da ya fi shahara a ƙabilar Igbo a zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata a watan Fabrairun 2023, Peter Obi, ya kasa cimma burinsa.

Ana sa ran Obi, wanda tsohon gwamnan jihar Anambra ne zai sake jaraba sa'arsa ta neman shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.

Primate Ayodele ya ce:

"Ba na ganin ɗan ƙabilar Igbo a matsayin shugaban ƙasa a 2027. Ko da duk ƴan ƙabilar Igbo sun haɗu, ba za su ba su shugabancin ƙasa ba."
"Igbo ba zai zama shugaban ƙasa ba."

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Gwamna Fubara ya sake kalubalantar Nyesom Wike

Ayodele Ya Yi Hasashen Juyin Mulki

A wani labarin kuma, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Ayodele Elijah Babatunde, ya yi hasashen yin juyin mulki a ƙasashen ECOWAS biyu.

Ayodele ya bayyana cewa ƙasashen ECOWAS guda biyu ne ya hasasowa juyin mulki nan ba da jimawa ba. Kasashen su ne Kamaru da kuma ƙasar Togo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel