Kotun Ɗaukaka Kara Ta Raba Gardama, Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Ɗan Majalisar Tarayya Daga Kaduna

Kotun Ɗaukaka Kara Ta Raba Gardama, Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Ɗan Majalisar Tarayya Daga Kaduna

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta bayyana hukuncin da ta yanke kan zaɓen ɗan majalisa mai wakiltar Jema'a da Sanga a majalisar tarayya
  • Kwamitin alkalan Kotun sun kori ƙarar da ɗan takarar APC ya kalubalanci nasarar Daniel Amos bisa rashin cancanta
  • Tun bayan kammala zaɓe a watan Fabrairu, INEC ta ayyana Amos a matsayin wanda ya samu nasara a mazaɓar ta Kaduna

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tabbatar da nasarar mamba mai wakiltar mazaɓar Jema’a/Sanga a majalisar wakilan tarayya, Daniel Amos.

Kotun daukaka kara ta yi hukunci a kujerar Jema’a/Sanga.
Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Nasarar Dan Majalisar Tarayya Daga Kaduna Hoto: channelstv
Asali: UGC

Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan ta yi fatali da karar da aka shigar gabanta wacce ta ƙalubalanci nasarar ɗan majalisar a zaɓen da aka yi a watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Bayan kwace kujerar Sanatan APC, Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan zaɓen Sanatan Kogi ta gabas

A hukuncin da suka yanke da murya ɗaya, kwamitin alƙalai uku na Kotun sun kori ƙarar da ɗan takarar APC, Usman Ato, ya shigar bisa rashin cancanta, Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da farko, hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Mista Daniel Amos, a matsayin wanda ya lashe kujerar ɗan majalisar Jema’a/Sanga a Kaduna.

Yadda aka fara shari'ar a Kotun zaɓe

Sai dai sakamakon rashin gamsuwa da hakan, Usman da jam'iyyar APC suka shigar ƙara gaban Kotun sauraron korafe-ƙorafen zaɓe, suka kalubalanci nasarar Amos.

Bayan tafka muhawara da baje kolin hujjoji, daga ƙarshe Kotun sauraron ƙarar zaben ƴan majalisar jiha da na tarayya ta Kaduna ta kori ƙarar bisa rashin cancanta.

Duk da haka bai haƙura ba, Usman Ato ya tunkari Kotun ɗaukaka ƙara inda ya zargi Mista Amos da amfani da takardun shaidar karatu na jabu.

Kara karanta wannan

Ndume da Lawal: Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan sahihancin nasarar Sanatocin arewa 2

Kotun ɗaukaka kara ta raba gardama

Alkalan Kotun ɗaukaka ƙara sun soki mai ƙarar da cewa dukkan zargin da yake a baki ne kawai domin babu wasu hujjoji da ya gabatar da zasu tabbatar da ikirarin da ya yi.

A cewar kotun, shaidun da wanda ya shigar da kara ya gabatar ba su taka kara sun karya ba, kuma ba za a iya amfani da su wajen soke zaben Mista Daniel Amos ba.

Emefiele ya samu nasara a Kotu

A wani rahoton kuma Wata Kotu a babban birnin tarayya Abuja ta bada umarnin gaggauta sakin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Ta ce a sake shi ba tare da gindaya masa wasu sharuɗɗa ba, inda ta umarci EFCC da shugaban hukumar su aiwatar da wannan umarni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel