Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Sahihancin Zaben Dan Majalisar Tarayya a NNPP, Jibrin

Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Sahihancin Zaben Dan Majalisar Tarayya a NNPP, Jibrin

  • Kotun daukaka kara ta raba gardama tsakanin dan takarar jam’iyyar NNPP da na APC a mazabar Kiru/Bebeji a jihar Kano
  • Kotun da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da nasarar Abdulmumin Jibrin na NNPP tare da fatali da karar Muhammad Kiru
  • A watan Satumba, har ila yau, kotun sauraran kararrakin zabe ta yi hukunci makamancin haka inda ta kori karar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Abdulmumin Jibrin na jam’iyyar NNPP a mazabar Kiru/Bebeji a majalisar Tarayya.

Kotun yayin yanke hukuncin ta yi fatali da karar Muhammad Said Kiru na jam’iyyar APC saboda rashin hujjoji.

Kotun zabe ta yi hukunc kan zaben Jibrin na jam'iyyar NNPP a Kano
Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan zaben Jibrin a Kano. Hoto: Abdulmumin Jibrin.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a Kano?

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan sahihancin zaben dan tsohon minista a jihar Neja

Kotun ta yanke hukuncin ne a jiya Laraba 1 ga watan Nuwamba inda Mai Shari’a, Anthony Ogakwu ya tabbatar da hukuncin kotun kararrrakin zabe da ta yi a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun har ila yau, ta ba da kyautar naira dubu 100 na dawainiya ga Jibrin na jam’iyyar NNPP, The Nation ta tattaro.

Kotun sauraran kararrakin zabe a watan Satumba ta kori karar Kiru da cewa ya gaza kawo hujjoji da za su wargaza zaben da aka gudanar.

Kotun ta kara da cewa takardun da mai karar da kuma wanda ake kara su ka gabatar a gaban kotun, sun ba da bayani iri daya.

Kotun ta kori karar Kiru a Kano

Takardun duka sun tabbatar da cewa Jibrin ya yi murabus a mukamin babban sakataren Hukumar Gidaje ta Gwamnatin Tarayya, Daily Post ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kano: Kujerar Majalisar Tarayya da kotu ta karbe ya dawo hannun NNPP a karshe

Ta ce hakan ya sabawa korafin da Kiru ya shigar da ya ke kalubalantar zaben da aka gudanar a watan Faburairu.

Wadanda aka maka kotun sun hada da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC da Abdulmumin Jibrin da kuma jam’iyyar NNPP.

Kotu ta tabbatar da Kingibe a matsayin Sanatar Abuja

A wani labarin, Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Ireti Kingibe ta jam’iyyar LP a matsayin wacce ta lashe zaben sanata a Abuja.

Kotun har ila yau, ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar a jam’iyyar PDP, Philip Tanimu Adudu na jam’iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel