Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Sahihancin Zaben Dan Tsohon Minista a Jihar Neja

Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Sahihancin Zaben Dan Tsohon Minista a Jihar Neja

  • Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari’ar zaben dan majalisar Tarayya a mazabar Lavun/Mokwa/Edati a jihar Neja
  • Dan takarar jam’iyyar APC a mazabar, Abdullahi Usman Gbatamagi na kalubalantar zaben Joshua Gana na jam’iyyar PDP
  • Kotun sauraran kararrakin zaben a watan Satumba ta yanke hukunci inda ta yi fatayi da hukuncin hukumar zabe da ta bai wa Gana nasara

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Neja – Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da nasarar Joshua Audu Gana na jam’iyyar PDP a mazabar Lavun/Mokwa/Edati a Neja.

Kotun ta yi watsi da hukuncin kotun sauraran kararrakin zabe da ta yi a ranar 11 ga watan Satumba.

Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan dan majalisar PDP a Neja
Kotu ta yanke hukunci kan shari'ar zaben dan majalisar Tarayya. Hoto: Joshua Gana.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a mazabar jihar Neja?

Kara karanta wannan

Kano: Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan sahihancin zaben dan majalisar Tarayya a NNPP, Jibrin

Yayin hukuncin karamar kotun, ta haramta satifiket da hukumar zabe ta bai wa Gana inda ta bukaci a sake gudanar da zabe a mazabun Lavun/Mokwa/Edati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, kotun daukaka karar a ranar Laraba 1 ga watan Oktoba ta tabbatar da korafin lauyan Gana, Akinola Kehinde da cewa karamar kotun ta yi kuskure a hukuncin.

Dan takarar jam’iyyar APC a mazabar, Abdullahi Usman Gbatamagi ne ke kalubalantar zaben Gana a kotun, cewar The Nation.

Wa yake kalubalantar zaben majalisar a kotun?

Kotun ta tabbatar da cewa Abdullahi na jam’iyyar APC ya saba ka’idar dokar zabe sakin layi ta 4 da 5.

Ta kara da cewa kotun sauraran kararrakin zabe ta tafka kuskure da ta ayyana Abdullahi na jam’iyyar APC da mallakar hujjojin da za su rusa zaben, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kano: Kujerar Majalisar Tarayya da kotu ta karbe ya dawo hannun NNPP a karshe

Gana shi ne mataimakin shugaban kwamitin wuta a majalisar wadanda aka nada a kwanakin baya.

Kotu ta tabbatar da nasarar Kingibe a matsayin sanatar Abuja

A wani labarin, kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Sanata Ireti Kingibe a matsayin wacce ta lashe zaben sanatan Abuja.

Ireti ta kasance ‘yar jam’iyyar LP wacce Sanata Philip Aduda na jam’iyyar PDP ke kalubalantar zabenta.

Kotun har ila yau, ta yi fatali da korafin Aduda saboda rashin gamsassun hujjoji na kare kararsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.