Gaskiya Ta Fito: Abdulmumin Jibrin Ya Tono Asirin Ganduje, Gwamnan Ya San Batun Ganawar Tinubu da Kwankwaso

Gaskiya Ta Fito: Abdulmumin Jibrin Ya Tono Asirin Ganduje, Gwamnan Ya San Batun Ganawar Tinubu da Kwankwaso

  • Abdulmumin Jibrin ya bayyana yadda Ganduje ya amince da ganawar Tinubu da Kwankwaso a baya
  • Ya ce, da sanin Ganduje zababben shugaban kasan ya gana da Kwankwaso a kasar Faransa a makon jiya
  • Akwai yiwuwar Kwankwaso da wasu ‘yan adawa su samu gata a mulkin Bola Ahmad Tinubu na APC

FCT, Abuja - Hon. Abdulmumini Jibrin, zababben dan majalisa ya ce, da izinin gwamna Abdullahi Umar Ganduje zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya gana da sanata Rabiu Musa Kwankwaso a Faransa.

A baya, rahotanninmu sun bayyana yadda Kwankwaso da Tinubu suka shafe sa’o’i hudu suna caccaka tsinke a ranar Litinin din da ta gabata, rahoton Daily Trust.

Ganduje ya san da batun ganawar Tinubu da kwankwaso
Ganduje, Tinubu da Kwankwaso | Hoto: Bola Tinubu, Abdullahi Ganduje, Rabiu Kwankwaso
Asali: Facebook

Ganduje dai ya nuna tashin hankali game da ganawar tasu, inda yace Tinubu ya gana da Kwankwaso ne don neman madadi.

Kara karanta wannan

Sharri aka min: Ganduje ya yi karin haske kan faifan muryarsa da ke yawo na sukar Tinubu

Ganduje ya yi katobara a faifan murya

A wani faifan muryar da aka yada, an ji Ibrahim Masari da Ganduje suna magana, inda yace Tinubu ya gana da Kwankwaso, lamarin da bai masa dadi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai, a wata tattaunawa da Daily Trust, Jibrin, wanda ke cikin wadanda suke tare da Ganduje a Faransa, ya ce Ganduje ya tabbatar masa cewa, Tinubu ya shawarce shi kafin ganawa da Kwankwaso.

Bayanai daga bakin Jibrin

Da yake martani game da faifan muryar, Jibrin ya ce:

“Kamar dai kowanne dan Najeriya, na kadu da sauraran faifan muryar amma ina tunanin abu mafi muhimmanci shine ina son tabbatar muku cewa an sanar da gwamna Ganduje.
“Kuma shi da kansa ya tabbatar min, ya sanar dani balo-balo cewa zababben shugaban kasa ya gayyace shi kuma ya fada masa cewa yana shirya ganawa da Kwankwaso kuma ya tambayi Ganduje ko yana da ja, kuma Gandujen dai ya shaida min ya cewa zababben shugaban kasa bashi da ja.”

Kara karanta wannan

To Fah: Kwankwaso, Wike da Wasu Yan Adawa 4 da Ka Iya Shiga a Dama Dasu a Mulkin Tinubu

Ganduje bai yiwa Tinubu adalci ba, inji Jibrin

Da yake karin haske game da yadda faifan muryar ke yaduwa, ya ce sam ba a yiwa Bola Tinubu adalci ba na bayyana shi a matsayin mayaudari.

Ya kara da cewa:

“Don haka ba daidai bane a ga laifin zababben shugaban kasa a bainar jama’a daga bakin Ganduje wanda ya san tabbas cewa shugaban ya nemi shawarinsa kafin ganawar saboda ya tabbatar min da hakan a bayyane.
“Ba kyautawa zababben shugaban kasa ba, kuma ban yi imanin cewa shugaban kasa zai yi watsi da duk wanda ya mara masa baya ba...amma duk da haka, abu mafi muhimmanci shine hadin kan kasa da ci gabanta.”

Tinubu zai iya ba Kwankwaso mukami a gwamnatinsa

A wani labarin, kunji yadda hasashe ya nuna wadanda za su iya tashi da kwabi a mulkin Bola Ahmad Tinubu.

An naqalto yadda ake sa ran ‘yan jam’iyyar adawa za su iya samun kujeru a mulkin na Tinubu, ciki har da Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Yadda Aka Ji Ganduje a Tarho Yana Kokawa Kan Zaman Tinubu da Kwankwaso a Faransa

Wannan lamari dai ya jawo sabuwar bullar tsama tsakanin Tinubu da Ganduje na jihar Kano da ke Arewa maso Yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel