Zaben Bayelsa: Jam'iyyar APC Ta Yi Magana Kan Cire Sunan Dan Takararta da INEC Ta Yi

Zaben Bayelsa: Jam'iyyar APC Ta Yi Magana Kan Cire Sunan Dan Takararta da INEC Ta Yi

  • Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba ta damu ba kan cire sunan Timipre Sylva da INEC ta yi daga cikin jerin ƴan takarar gwamnan Bayelsa
  • APC a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa wannan wani koma baya ne na wucin gadi sannan ta buƙaci magoya bayanta su kwantar da hankulansu
  • Jam'iyyar ta yi nuni da cewa lauyoyinta na kotu domin ganin an kawar da hukuncin hana Sylva shiga cikin zaɓen na ranar 11 ga watan Nuwamba

Jihar Bayelsa - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta mayar da martani kan cire sunan ɗan takararta Timipre Sylva daga cikin jerin sunayen ƴan takarar gwamnan jihar Bayelsa, cewar rahoton PM News.

A ranar Talata ne dai hukumar INEC ta fitar da sunayen ƴan takarar gwamnan da za su fafata a zaɓen na ranar, 11 ga watan Nuwamba, inda ba a ga sunan Timipre Sylva ba, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Assha: Yadda Rashin Jituwa Ta Sanya Magidanci Ya Halaka Matarsa da Wuka

APC ta magantu kan cire sunan Sylva
APC ta yi martani bayan INEC ta cire sunan Sylva daga cikin yan takara Hoto: Timipre Marlin Sylva
Asali: Facebook

INEC ta cire sunan Slyva ne saboda hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke na hana shi shiga zaɓen.

Wane martani jam'iyyar APC ta yi?

Sai dai, da yake mayar da martani kan hakan, darektan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaben gwamnan jihar Bayelsa na APC, Mista Perry Tukuwei, a cikin wata sanarwa ranar Laraba, ya ce wannan wani koma baya ne na wucin gadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma buƙaci magoya bayan jam'iyyar da ka da su tayar da hankulansu kan cire sunan Sylva da aka yi.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnan APC na jihar Bayelsa na kira ga mutanen mu na jihar Bayelsa da ka da gwiwoyinsu su yi sanyi kan abubuwan da ke faruwa a cikin ƴan kwanakin nan yayin da muka tunkari nasara a zaɓen ranar 11 ga watan Nuwamba."

Kara karanta wannan

Fintiri Vs Binani: Magana Ta Kare, Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Sahihancin Zaben Gwamnan Adamawa

"Mutanen mu na jihar Bayelsa, ka da ku sanya tsoro. Ka da ku sare. Muna kan hanya babu wani abu da zai ɗauke mana hankali."

APC ta ɗaukaka ƙara

Ya ƙara da cewa:

"Lauyoyinmu suna kula da komai, muna sa ran samun nasara a kotun ɗaukaka kara. Za mu yi nasara.”

Jam'iyyar APC dai ta shigar da ƙara inda take kalubalantar hukuncin kotun sannan ta nemi a ɗage aiwatar da hukuncin har zuwa lokacin da za a yanke hukunci.

Rikici Tsakanin Minista da Shugaban Majalisa

A wani labarin kuma, mataimakin shugaban majalisar wakilai ta ƙasa, Benjamin Kalu, ya bayyana cewa babu wata rigima tsakaninsa da ƙaramar ministar ƙwadago da ayyuka, Nkeiruka Onyejeocha.

Kalu ya bayyana cewa akwai alaƙa mai kyau tsakaninsa da ministar ta Shugaba Bola Ahmed Tnubu, saɓanin yadda aka raɗe-raɗen suna rikici a tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel