El-Rufai: Tinubu Ya Shirya Magance Matsalar Wutar Lantarki a Cikin Shekara 7

El-Rufai: Tinubu Ya Shirya Magance Matsalar Wutar Lantarki a Cikin Shekara 7

  • Malam El-Rufai ya burge jama’a tun wajen jero makarantun da ya halarta domin samun digiri da digirgir
  • Abdulaziz Yari ne ya yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna tambayoyi, kuma an ji gamsassun amsoshi
  • El-Rufai ya yi wa majalisa bayanan yadda zai bunkasa bangaren wutar lantarki idan ya zama Minista

Abuja - An cigaba da tantance Ministocin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aikowa Majalisar Dattawa, a yau Talata aka shiga rana ta biyu.

Legit.ng Hausa ta bibiyi tantance Ministocin, Nasir Ahmad El-Rufai yana cikin wadanda su ka je gaban Sanatoci kamar yadda aka taba yi a 2003.

Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya fara bayyana kan shi tun daga haihuwarsa kauyen Daudawa a Katsina da kuma tashinsa a Kaduna zuwa samun mulki.

El-Rufai
Ministoci: An tantance El-Rufai a Majalisar Dattawa Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

An yi gaba-da-baya a Majalisa

Sanata Ibrahim Khalil ya yi magana a madadin Sanatocin Kaduna, ya ce sun amince tsohon Gwamnan ya zama Minista ba tare da yi masa tambaya ba.

Kara karanta wannan

Malaman Addinin Musulunci a Arewa Sun Roki a Hana El-Rufai Yin Minista, Sun Bayyana Dalili

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da Sanatan Kogi ta yamma ya yabi Malam El-Rufai, sai dai ya nuna akwai korafi a kan shi, tuni Sanata Muhammad Sani Musa ya maida masa raddi.

Abdulaziz Yari ya yi wa tsohon Gwamnan Kaduna tambayoyi uku kan yadda zai kawo gyara a Najeriya idan ya samu kan shi a bangaren lantarki.

Amsoshin Nasir El-Rufai

El-Rufai ya dauki lokaci ya amsa yadda zai gyara harkar wuta idan wanda a nan ya burge mutane.

Kwararren ‘dan siyasar ya kawo matsalar karancin gas, lamarin siyasa, rashin kayan aiki a cikin abubuwan da su ka jawo aka gaza samun isasshen wuta.

Shi da kan shi ya yarda matsalar ta nemi ta gagari kowane shugaban kasa, yana mai cewa Bola Tinubu ya na son magance matsalar nan da shekara bakwai.

A cewarsa, Mai girma shugaban kasa ya zauna da shi domin ganin an samu mafita, ya kuma nuna takaici kan yadda irinsu Benin su ke da wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Bidiyon Tinubu Yana Rokon El-Rufai a Fili, Ya Karbi Mukami Idan An Kafa Gwamnati

Kafin a iya yin gyara, El-Rufai ya ce sai an hada-kai da ‘yan majalisa da sauran al’umma, kamar yadda ake bukatar a gyara dokokin wuta da na lantarki.

Tun daga yadda aka saida kamfanonin lantarki, tsohon Ministan na Abuja ya fede matsalar tare da yin bayanin yadda za a jawo kwararru da nufin yin gyara.

An tantance David Umahi

Dazu kun ji labari wanda aka fara da shi a ranar Talata shi ne Sanata David Umahi wanda ‘dan majalisar dattawa ne da yake shirin zama Minista.

David Umahi ya bayyana kan shi ta hanyar jero ayyukan da ya yi a matsayin shugaban jam’iyya zuwa Gwamnan Ebonyi da kuma Majalisa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel