
AbdulAziz Yari







Sammako Sanatoci su ka yi wajen zuwa majalisar tarayya a ranar da za ayi zabe. Sanatan Ekiti ya ce sun yi kwanaki babu barci saboda yakin zaben Akpabio/Barau.

Za a ji dalilan da su ka jawowa Abdulaziz Yari cikas a zaben Majalisar Dattawan Najeriya. Tun daga Jam'iyya har zuwa fadar shugaban kasa, ba su tare da Yari.

Za a ji labari tsohon Ministan Neja-Delta, Sanata Godswill Akpabio ya lashe zaben majalisar dattawan Najeriya da aka yi a safiyar Talata, 13 ga watan Yuni 2023.

Bangaren Sanata Abdulaziz Yari, ɗaya daga cikin na gaba-gaba a takarar shugabancin majalisar dattawa, ya musanta zargin yin amfani da kudi domin siye sanatoci.

Kungiyar Fastoci da Limamai na Kiristoci ta bayyana goyon bayanta ga shugabancin Abdulaziz Yari a majalisar dattawa ta 10, kungiyar ta ce yafi kowa dacewa.

Sanata Abdul Ningi ya ce mambobi 67 ne ke bayan Abdulaziz Yari a kokarinsa na zama shugaban majalisar dattawa, ya ce ya kamata a bari mambobin su zabi ra'ayinsu

Zababben Sanata da zai wakilci Zamfara ta yamma a majalisar dattawa, Abdulaziz Yari ya ki jin lallashi, ya ce Ubangiji kadai zai zabi sabon Shugaban Majalisa.

Sanata Abdulaziz Yari Abubakar ya kai wa tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ziyara a gidansa da ke Daura, jihar Katsina. Ziyarar dai na da alaka.

Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a birnin tarayya Abuja, ta hana hukumomin EFCC, ICPC da DSS daga cafke tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari.
AbdulAziz Yari
Samu kari