Shugaban APC Na Jihar Arewa Ya Yi Murabus Awanni Bayan Nada Ganduje

Shugaban APC Na Jihar Arewa Ya Yi Murabus Awanni Bayan Nada Ganduje

  • Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar ya yi murabus daga kan kujerarsa
  • Haliru Jikantoro, wanda ya kasance shugaban APC a jihar ta arewa maso tsakiya, ya bayyana shawarar da ya yanke a gaban hadimansa
  • Alhaji Aminu Musa, shugaban APC a yankin 'Zone 'C' shine zai maye gurbin Jikantoro a matsayin mukaddashin shugaba

Minna, Jihar Niger - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Haliru Zakari Jikantoro, ya yi murabus daga kan kujerarsa.

Shugaban jam'iyyar na APC ya yanke shawarar ne a bainar jama'a ba tare da bayyana wani dalili ba.

Shugaban APC a jihar Neja ya yi murabus
Da Dumi-Duminsa: Shugaban APC Ya Yi Murabus, Bai Fadi Dalili Ba Hoto: Musa D Sarkinkaji
Asali: Facebook

Shugaban APC a jihar Neja ya yi murabus

Ya sanar da murabus dinsa bayan wata ganawa da kwamitin aiki na jam'iyyar a jihar a sakatariyar APC da ke garin Minna, a gaban babban mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Mohammed Nma Kolo, TVC News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Fadi Dalilin Ƙin Halartar Taron da Ganduje Ya Zama Sabon Shugaban APC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron, Jikantoro ya kuma sanar da mataimakin shugaban jam'iyyar a Neja ta arewa, Alhaji Aminu Bobi, a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar.

Ya kuma nuna yakinin cewa ficewarsa zai kawo ci gaba ga jam'iyyar a jihar, rahoton Daily Trust.

Jikantoro ya ce:

"Ina ganin ya zama dole kuma ya zama wajibi a gare ni na kira taron gaggawa don yi wa shugabannin jam'iyyar a jihar bayani, da kuma abin da ya faru jiya (Alhamis, 3 ga watan Agusta). Abu na daya kenan; wanda na yi.
"Abu na biyu, Ni, a nawa karan kaina, na yi muradin yin murabus daga mukamina, a matsayin shugaban jam'iyyar APC a jihar Neja.
"Wannan ne dalilin da yasa na yanke shwarar gayyata kafofin watsa labarai da su zo su nadi wannan taron."

Kara karanta wannan

Ta Fasu: Jiga-Jigan APC Sun Tona Asirin Wike, Sun Faɗi Dalilinsa Na Haɗe Wa da Shugaba Tinubu

Ya kara da cewar:

"Babu matsaloli ko rikici, Ina ganin zan iya kawo ci gaba a wasu mukaman a nan gaba."

Gwamnan Benue Ya Gana da Shettima Kan Batun Samar da Isasshen Abinci

A wani labarin, Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai, a ranar Alhamis ya bukaci gwamnatin tarayya da ta ba da fifiko wajen bunkasa harkar noma domin taimaka wa Najeriya ta samu wadatar abinci.

Ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai na gidan gwamnati jim kaɗan bayan ganawa da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wannan gana wa da ta gudana a fadar shugaban ƙasa ta zo ne jim kaɗan bayan sun halarci taron majalisar zartarwan APC ta ƙasa (NEC).

Asali: Legit.ng

Online view pixel