Abba Gida Gida Ya Ce Babu Nadama Kan Rushe-Rushen Da Gwamnatinsa Ke Yi a Kano

Abba Gida Gida Ya Ce Babu Nadama Kan Rushe-Rushen Da Gwamnatinsa Ke Yi a Kano

  • Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce babu nadama kan aikin rusau da gwamnatinsa ke yi
  • Ya ce hakan na daga cikin alƙawuran da ya ɗaukawarwa 'yan jihar Kano a lokacin ƴaƙin neman zaɓe
  • Mai magana da yawun gwamnan jihar, Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana haka a hirarsa da gidan rediyon Freedom

Kano - Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa babu nadama akan rushe-rushen da gwamnatinsa ke gudanarwa a jihar.

Mai magana da yawun gwamnan, Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan a hirarsa da rediyon Freedom, cikin shirinsu na Kowane gauta na ranar Laraba.

Ya ce rusau ɗin da Abba yake gudanarwa a yanzu duk gyara ne kuma al'ummar da suka zaɓi gwamnati suna maraba da shi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Yi Tonon Silili, Ya Bayyana Ainihin Masu Kashe Al'umma a Jiharsa

Gwamnatin Kano ta ce ba ta nadama kan rushe-rushen da ke gudana a Kano
Abba Gida Gida ya ce ba ya nadama kan rushe-rushen da ke gudana a Kano: Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alƙawarin da Abba Gida Gida ya ɗaukarwa al'ummar jihar Kano kenan

Sunusi Bature ya ce tun a lokacin yaƙin neman zaɓe, Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin dawo da taswirar jihar Kano kamar yadda take a baya.

Ya ƙara da cewa da aka zo zaɓe, al'ummar jihar Kano sun zaɓi Abba wanda hakan ke nuni da cewa sun amince da wannan ƙuduri da ma wasu sauran ƙudururrika masu amfani.

A domin haka ne Sunusi ya ce ya zama wajibi Abba ya cikawa mutanen Kano da suka zaɓe shi wannan alƙawari da ya ɗauka.

Ayyukan da Abba Gida Gida ya yi a cikin kwanaki 40 ɗinsa na farko

Sunusi ya kuma bayyana cewa, a duk sanda sabuwar gwamnati ta zo akan samu gyare-gyare da ma wasu sabbin abubuwa, inda ya ce an samu nasarori da dama a cikin kwanaki 44 da gwamnatin Abba Gida Gida ta shafe a kan mulki.

Kara karanta wannan

Daga Karshe El-Rufai Ya Bayyana Gaskiyar Ma'anar Kalaman Da Ya Yi Kan Hanyar Da Shugaba Tinubu Ya Ci Zabe

Ya ce daga cikin ayyukan da Abba Gida Gida ya yi akwai gyaran fitilun kan hanya domin magance matsalar ƙwacen waya da Kano ke fama da shi.

Sunusi ya ƙara da cewa akwai batun shara da ta addabi jihar Kano, wacce yanzu haka ake kwashewa kuma ana kai ta inda ya dace.

Ya kuma ce akwai batun biyan kuɗin ɗalibai na kammala jarabawar sakandire wacce Abba ya biya duka kuɗaɗen saɓanin gwamnatin baya da ta daina biya.

Abba Ya Mayar Da Daurawa Kan Muƙaminsa na shugabancin hukumar Hisbah

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mayar da Sheikh Aminu Daurawa muƙaminsa na shugabancin hukumar Hisbah ta jihar Kano.https://hausa.legit.ng/news/1543508-gwamnan-kano-ya-mayar-da-daurawa-kan-mukaminsa-na-shugaban-hisbah-ta-kano/

Sheikh Daurawa ne ya tabbatar da hakan a hirarsa da manema labarai a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel