Buhari Ya Yi Jawabi da Jin Tinubu Ya Zama Sabon Shugaban Kungiyar ECOWAS

Buhari Ya Yi Jawabi da Jin Tinubu Ya Zama Sabon Shugaban Kungiyar ECOWAS

  • Muhammmadu Buhari ya taya Bola Tinubu murnar zama sabon Shugaban kungiyar ECOWAS
  • A jiya ne ysohon shugaban Najeriya ya fitar da jawabi na musamman ta bakin Malam Garba Shehu
  • Mai magana da yawun Buhari yana fatan kasashen Yammacin Afrika su samu cigaba a lokacin Tinubu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Muhammadu Buhari ya fitar da jawabi na musamman bayan samun labari Bola Ahmed Tinubu ne zai jagoranci kungiyar ECOWAS.

The Cable ta kawo labari a ranar Litinin cewa Muhammadu Buhari ya taya Shugaba Bola Ahmed Tinubu murnar wannan matsayi da ya samu.

A karshen makon nan kungiyar kasashen yammacin Afrika ta zabi shugaban Najeriya ya zama sabon shugabanta, ya gaji Umaro Embalo.

Tinubu Buhari ECOWAS
Muhammadu Buhari ya taya Tinubu murna Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

Buhari wanda ya yi mikawa Tinubu mulki a Mayu ya fitar da jawabi ya na fatan yammacin Afrika ta samu cigaba a karkashin jagorancinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Dawo Najeriya, Gbajabiamila da Ganduje Sun Tarbo Shi a Filin Jirgi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake magana ta bakin Garba Shehu, tsohon shugaban Najeriyan ya yi fatan kungiyar nan ta dawo da martabatarta a zamanin magajinsa.

Daily Nigerian ta rahoto Malam Shehu ya na fadawa Tinubu cewa babban nauyi aka ba shi.

Jawabin da Muhammadu Buhari ya fitar

“Mutanen Yammacin Afrika sun daura tulin nauyin jagorantarsu a kan sabon shugabanmu.
Aikinmu ne a matsayin ‘yan kasa mu mara masa baya, kuma ka da mu ba shi kunya.
Ina rokon Ubangiji Madaukaki ya sa wa’adinsa a matsayin shugaban shugaban kasashe da gwamnatoci ya dawo da martabar ECOWAS a matsayin jagorar damukaradiyya, shugabanci na kwarai kuma ginshiki wajen yaki da ta’addanci da sauyin yanayi a nahiyar.”

- Muhammadu Buhari

Tuni dai har Tinubu ya karbi wannan aiki da aka ba shi kwanaki 41 bayan zamansa shugaban Najeriya a sakamakon lashe zabe da ya yi a bana.

Kara karanta wannan

Obasanjo, Buhari, IBB Da Lokuta 9 Da Shugaban Najeriya Ya Zama Shugaban ECOWAS

Shugabannin ECOWAS a tarihi

Ku na da labari Muhammadu Buhari ne ya yi dacen zama Shugaba sau biyu a tarihi, a 1980s da kuma 2018-2019 bayan ya dawo mulkin farar hula.

Daga 1985 zuwa 1999, Najeriya ta ke rike da ECOWAS, shekaru 14 kenan a jere. Janar Sani Abacha da Umaru Yaradua sun taba jan ragamar kungiyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel