KARIN BAYANI: Rudani Yayin Da Rahoto Ya Yi Ikirarin Tinubu Ya Yi Nade-Naden Farko Bayan Rantsarwa

KARIN BAYANI: Rudani Yayin Da Rahoto Ya Yi Ikirarin Tinubu Ya Yi Nade-Naden Farko Bayan Rantsarwa

  • An shiga ruɗani game da wani rahoto wanda ya yi ikirarin shugaban ƙasa Tinubu ya yi naɗe-naɗen farko a sabuwar gwamnatinsa
  • Rahoton ya nuna cewa Tinubu ya naɗa shugaban tsare-tsaren ofishinsa, kakakin shugaban ƙasan da kuma mai ba da shawara kan digital midiya
  • A ɗazu ne shugaban kasan ya karbi shahadar kama aiki bayan wa'adin Buhari ya kare a filin wasa na Eagle Square Abuja

Abuja - Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa ya yi ikirarin cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi naɗe-naɗen farko bayan hawa gadon mulki ranar Litinin 29 ga watan Mayu, 2023.

A rahoton jaridar, shugaba Tinubu, wanda bai jima da karban rantsuwar kama aiki ba ya naɗa Ambasada Kunle Adeleke a matsayin SCOP a taƙaice (State Chief of Protocol).

Kara karanta wannan

A Ranar Farko, Shugaba Tinubu Ya Ɗauki Mataki Mai Kyau Kan Sauya Takardun Naira

Bola Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Sanar da Nada Mutum 3 a Karon Farko Bayan Karban Mulki Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Haka zalika Bola Tinubu ya naɗa tsohon kwamishinan yaɗa labarai a jihar Legas, Dele Alake, a matsayin kakakin shugaban ƙasa da kuma Olusegun Dada a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan digital Midiya.

Sai dai a halin yanzun jaridar ta goge rahoton kwata-kwata daga shafinta kuma ba tare da wata sanarwa a hukumance ba kan wannan ci gaban.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sabon shugaban kasan, ya yi waɗan nan sabbin naɗe-naɗe ne jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin zababben shugaban ƙasa na 16 a tarihin Najeriya.

Su wa ake tunanin zasu shiga gwamnatin Tinubu?

Kafin yau, ana ta yaɗa jita-jita kan su wa sabon shugaban ƙasan zai fara naɗa wa a gwamnatinsa bayan ya shiga ofis ɗin mutum lamba ɗaya a Najeriya.

Tun da safiya, sakataren kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a inuwar APC, James Abiodun Faleke, ya sanar da cewa akwai ruɗani game da waɗanda ake tsammani zasu fara hawa motar mulkinn Tinubu.

Kara karanta wannan

Rantsar Da Tinubu: Muhimman Abubuwa 3 Da Yakamata Ku Sanya Ido Akai a Ranar 29 Ga Watan Mayu

Sai dai Faleke ya ce yana tsammanin Tinubu zai gama naɗe-naɗensa cikin kwanki 60 da shiga Ofis, inda ya kafa hujja da sabuwar doka wacce tsohon shugaban ƙasa ya rattaɓa wa hannu.

Zan Sake Nazari Kan Tsarin Sauya Fasalin Naira da Buhari Ya Yi, Shugaba Tinubu

A wani rahoton na daban Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taɓo tsarin canja takardun naira a jawabinsa na wurin rantsarwa.

Sabon angon Najeriya ya zai sake nazari kan tsarin wanda Buhari ya kawo a zamanin mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel