El-Rufai Ya Soke Lasisin Hakkin Mallaka Na Kamfanoni 9, Zai Rushe Su a Kaduna

El-Rufai Ya Soke Lasisin Hakkin Mallaka Na Kamfanoni 9, Zai Rushe Su a Kaduna

  • Gwamna Malam Nasiru El-Rufai ya waiwayi kadarorin tsohon gwamnan Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi
  • El-Rufai ya kwace shaidar hakkin mallaka kana ya soke lasisin kamfanoni 9 duk mallakin tsohon gwamnan
  • Makarfi ya tabbatar da cewa takardun Notis sun shigo hannunasa amma ya fara kokarin ɗaukar matakin doka kan lamarin

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya soke lasisin haƙƙin mallaka na wasu Kamfanoni 9 mallakin tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmed Makarfi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamna El-Rufai ya shafa wa baki ɗaya kadarorin da lamarin ya shafa fentin da ke nuna gwamnati na shirin rushe su.

Kaduna.
El-Rufai Ya Soke Lasisin Hakkin Mallaka Na Kamfanoni 9, Zai Rushe Su a Kaduna Hoto: The Governor Of Kaduna
Asali: Facebook

Bayanai sun nuna cewa tuni gwamnatin Malam El-Rufai ta aike da wasiƙar soke lasisi da kuma janye haƙƙin mallaka ga shugabannin kamfanonin da lamarin ya shafa.

A wasikun da gwamnatin Kaduna ta aike wa kamfanonin 9 ɗauke da sa hannun shugaban hukumar tattara bayanan filayen Kaduna (KADGIS), Mahmud Aminu, ya ce:

Kara karanta wannan

An Fara Musayar Yawu Tsakanin Gwamnatin Buhari da Gwamnan APC Kan Satar Kuɗin Talakawa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"An umarce ni na sanar muku da cewa mai girma gwamna Malam Nasiru El-Rufai, bisa dogaro da karfin ikon da sashi na 28 (5) (a) da (b) na kundin dokokin mallakar ƙasa 1978 ya ba shi, ya soke tare da janye haƙƙin mallakarku."

Makarfi ya bayyana matakin da zai ɗauka

Da yake martani kan batun yayin amsa sakon da aka tura masa ta wayar tarho, Sanata Makarfi, ya tabbatar da cewa wasiƙun soke lasisin sun iso gare shi.

The Cable ta rahoto Makarfi na cewa:

"Akwai matsala babba, muna kokarin haɗuwa da Ustaz Yunus (SAN) domin mu garzaya Kotu ta dakatar da gwamnatin Kaduna, yanzu suka aiko mana da wasikar sokewa guda 9."

Daga cikin kadarorin Makarfi da gwamna El-Rufai ya biyo ta kansu a yanzu sun haɗa da Feguna 5 a Magadishu, Uku a Titin Kwato da kuma guda ɗaya a Doka.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Ba Da Belin Sheikh Idris Dutsen Tanshi, Ta Gindaya Sharuɗda

Kwanaki 10 suka rage wa Malam Nasiru El-Rufai a kan gadon mulki, zai sauka ranar 29 ga watan Mayu, bayan shafe zango biyu a kan madafun iko.

Majalisa Ta 10: Gwamnonin Arewa Na APC Ba Zasu Saba Wa Tinubu Ba, Sule

A wani rahoton na daban kun ji cewa Gwamnonin arewa na jam'iyya mai mulki sun cimma matsaya kan shugabancin majalisar tarayya ta 10.

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce da zaran zababben shugaban ƙasa ya dawo Najeriya zasu zauna da shi kan muhimmin abu 1.

Asali: Legit.ng

Online view pixel