Jihar Bauchi: An Sako Sheikh Idris Duten Tanshi Daga Gidan Yari

Jihar Bauchi: An Sako Sheikh Idris Duten Tanshi Daga Gidan Yari

  • Bayan shafe kwana ɗaya a gidan Yari, Kotu ta amince da bukatar Belin Dakta Idris Dutsen Tanshi, jihar Bauchi
  • A jiya Litinin hukumar yan saɓda ta gurfanar da Malamin bisa zargin kalaman da ka iya tunzura jama'a
  • Sai Alkali ya umarci a tsare shi a gidan Yari zuwa yau Talata gabanin yanke hukunci kan buƙatar beli

Bauchi - Bayan shafe kwana ɗaya a gidar Kurkuku, an sako shahararren Malamin Addinin Musuluncin nan, Sheikh Dakta Idris Abdu'aziz Dutsen Tanshi, jihar Bauchi.

Shafin Dabo TV ne ya tabbatar da sako fitaccen Malamin kuma babban limamin Masallacin Jumu'a na Dusten Tanshi, a wani bidiyo da ya wallafa a Facebook.

Dr. Idris Dutsen Tanshi.
Jihar Bauchi: An Sako Sheikh Idris Duten Tanshi Daga Gidan Yari Hoto: BBC
Asali: UGC

A bidiyon da ta wallafa, Sheikh Sani Al-Kanawi, ya ce:

"Muna kara godiya ga Allah, Allah mai girma, yan uwa a yanzu haka cikin ƙoshin lafiya da aminci, Dakta (Dr Idris Abdu'aziz) yanzu haka ya fito, muna ƙara yi wa Allah godiya."

Kara karanta wannan

Rai Ya Yi Halinsa Yayin Da Fada Ta Barke a Tsakanin Jami'an EFCC a Sokoto

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotu ta ba da belin Malam Idris

BBC Hausa ta rahoto cewa a ranar Talata (Yau) Kotun Majirtire ta amince da ba da belin shahararrren Malamin yayin da take yanke hukunci kan buƙatar da lauyoyinsa suka gabatar.

Da farko dai lauyoyin Malamin su faɗa wa Kotun cewa tuhumar da ake wa Sheikh Idris ba zata hana a bayar da belinsa ba dogaro da tanade-tanaden kundin dokokin ƙasar nan.

Kotu ta kafa sharuddan Beli

Ɗaya daga cikin lauyoyin da suka tsaya wa Malamin, Barista Alƙassim Muhammad, ya bayyana cewa Kotu ta amince da buƙatar beli amma ta gindaya sharuɗɗa.

A cewar lauyan, abu na farko dole Dakta Idris ya gabatar da waɗanda zasu tsaya masa mutum biyu, ma'aikacin gwamnati da ya kai matsayin babban Sakatare da kuma Basarake.

"Abu na biyu, mutanen zasu gabatar da takardar shaidar mallakin wata kadara mai darajar aƙalla miliyan N5m a gaban Kotu," inji Lauyan.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Kan Mutane a Arewa, Gwamnan APC Ya Fusata Ya Ɗau Mataki

Bugu da ƙari, Kotu ta nemi duk waɗanda zasu tsaya wa Malam Idris su gabatar da Hotunansu ga Rijistara kafin a saki Dakta Dutsen Tanshi.

Gwamnatin Buhari Samar da Sabbin Ayyuka Miliyan 12m a Najeriya

A wani labarin kuma A Ɓangare Ɗaya Rak, Shugaba Buhari Ya Samar da Ayyukan Yi Ga Yan Najeriya Miliyan 12m

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa gwamnatin Buhari ta baiwa maraɗa kunya a tsawon shekaru 8 da ta shafe kan madafun iko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel