Dalilin da Yasa Orji Kalu Ba Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa Ba, Adamu

Dalilin da Yasa Orji Kalu Ba Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa Ba, Adamu

  • Ana ganin tsohon gwamnan jihar Abiya, Sanata Orji Kalu, zai janye daga takarar shugaban majalisar dattawa ta 10
  • Babban jigon APC, Adamu Garba, ya ce Kalu ba zai iya cin zaben shugaban majalisa ba saboda jam'iyya ba ta taɓuka komai ba a Kudu maso Gabas
  • Sai dai magoya bayan Kalu sun kafe cewa Kudu maso Gabas ya dace APC ta miƙa kujarar shugaban majalisar dattawa

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar YPP kuma jigon jam'iyyar APC a yanzu, Adamu Garba, ya faɗi kalamai masu jan hankali kan burin Orji Uzo Kalu na neman kujerar shugaban majalisar dattawa.

Jigon APC ya ce mai yuwuwa tsohon gwamnan jihar Abiya, Sanata Kalu, ya cancanci zama a kujerar amma duk da haka ba zai samu nasarar shugabancin majalisar dattawa ta 10 ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn a Asusun Jihar Domin Siyo Motocin Kece Raini

Adamu Garba da Orji Kalu.
Dalilin da Yasa Orji Kalu Ba Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa Ba, Adamu Hoto: @adamugarba, Orji Kalu
Asali: Facebook

A cewar Adamu Garba, Sanata Kalu ba zai kai labari ba saboda ƙarancin ƙuri'un da shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya ta baiwa APC a babban zaben 2023 da aka kammala.

Babban jigon jam'iyya mai mulki, Adamu, ya faɗi haka ne ranar Litinin 15 ga watan Mayu, 2023 yayin da ya bayyana a cikin shirin Arise TV mai suna, "Morning Show."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma bayyama cewa yana ganin mai ladabtarwa na majalisar dattawa ta tara zai fito ya faɗawa yan Najeriya cewa ya janye daga takara a majalisa ta 10.

A kalamansa, Adamu Garba ya ce:

"Ina ji a raina Sanata Orji Kalu zai janye daga tseren kujerar shugaban majalisar dattawa. Ya cancanci muƙamin amma idan muka tsaya muka duba, Kudu maso Gabs bata tabuka komai ba."
"Shawarata ya tashi tsaye ya lalubo hanyoyin haɗo kan mutanen Kudu maso Gabas, saboda nan gaba APC ta ƙara karfi a shiyyar."

Kara karanta wannan

"Dalilin Mu Na Bijirewa Matsayar APC Kan Shugabancin Majalisa Ta 10", Betara Ya Fasa Kwai

Bidiyon hira da Adamu Garba ya watsu a soshiyal midiya

Kotu ta tsige hadimai 18 a NDDC

A wani labarin kuma Kotu Ta Tsige Hadimai 18 da Shugabar NDDC Ta Nada Ba Bisa Doka Ba

Babbar kotun tarayya ta tunbuke hadiman da shugabar hukumar raya Neja Delta ta naɗa, ta ce ta shiga aikin da ba nata ba.

Bayan haka Kotun ta haramtawa shugabar shiga aikin daraktan gudanarwa, wansa hakkinsa ne ɗaukar hadiman aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel