Matashi Ya Zama Zababben ‘Dan Majalisar Wakilai Yana ‘Dan Shekara 29 da Haihuwa

Matashi Ya Zama Zababben ‘Dan Majalisar Wakilai Yana ‘Dan Shekara 29 da Haihuwa

  • Wanda zai zama sabon ‘Dan majalisar mazabar Mbaitoli/ Ikeduru, matashi ne ‘dan kasa da shekara 30
  • A zaben da hukumar INEC ta karasa a Jihar Imo, Akarachi Amadi ya samu kuri’u fiye da 20, 000
  • Mbaitoli/ Ikeduru sun samu wakilcin matashi kamar yadda aka samu a B/Kebbi, Godo/Goranyo

Imo - Akarachi Amadi wanda ake maganar bai wuce shekaru 28 da 29 ba, shi ne zai zama ‘dan majalisar mazabar Mbaitoli/ Ikeduru a jihar Imo.

Daily Trust ta ce Akarachi Amadi ya yi nasara a zaben majalisar wakilan tarayyar ne bayan sakamakon karashen zaben ya fito a ranar Lahadi.

Hukumar INEC ta tabbatar da nasarar ‘dan takaran na jam’iyyar PDP a zaben ranar Asabar. Wannan ya jawo mutane suka shiga bikin farin ciki.

Punch ta ce Baturen zaben, Farfesa Boniface Okoro ya bada sanarwar sakamakon a ofishin INEC na Nworuibi a karamar hukumar Mbaitoli a Imo.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An shiga tashin hankali, shugaban APC a wata jiha ya fadi matacce

Yadda jam'iyya APC ta ci zabe

Farfesa Okoro yake cewa wanda ya fi kowa yawan kuri’u a zaben shi ne ‘dan takaran APC wanda ya samu kuri’u 21, 372, ya doke ‘dan jam’iyyar LP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Uche Ogbuagu wanda ya tsaya takara a LP ya samu kuri’u 18, 296. Shi kuwa wanda yake rike da kujerar APGA, Henry Nwawuba ya kare ne da 7, 202.

Akarachi Amadi
Akarachi Amadi Hoto: koko.ng
Asali: UGC

Jam’iyyar PDP ta zo ta hudu bayan ‘dan takaran da ta tsaida, Usmond Ukanacho ya samu kuri’u 6, 681, yana gaban jam'iyyun ADC da SDP.

Modestus Osakwe ya ci kujerar Isu

Jaridar ta kuma ce Modestus Osakwe ya samu kujera a majalisar dokokin Imo, hakan ya ba shi daman zaman ‘adawa tal a cikin ‘yan majalisar jihar.

Mai magana da yawun bakin hukumar INEC ta reshen Imo, Dr Chinenye Chijioke Osuji ta shaidawa manema labarai cewa Osakwe ya ci zabe.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa: APC ta lashe kujeru 59, an fadi yawan na PDP, NNPP, LP da SDP

Jam’iyyar adawar ta ji dadin jin wannan labari, take cewa nasarar ta tabbatar da akwai haske, tare da yabon Osakwe da cewa mazabarsa tayi dace.

A zaben bana, an samu matasa da za a rantsar a majalisa daga jihohin Kebbi, Sokoto da Imo.

Lallai Allah SWT ne yake bada mulki

Rahoto ya zo a baya cewa tsohon Kwamishinan Gwamna Aminu Tambuwal, Bashir Usman Gorau ya doke wanda ya yi shekaru 16 a Majalisar tarayya.

Kafin PDP ta kawo karshensa, Musa S Adar ya lashe zabukan majalisa na 2007, 2011, 2015 da 2019, yana cikin manyan majalisa da suka rasa tazarce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel