“Ku Tafi Kotu Sannan Ku Jira Hukunci”: Buhari Ga Atiku, Obi Da Sauran Wadanda Suka Fadi Zabe

“Ku Tafi Kotu Sannan Ku Jira Hukunci”: Buhari Ga Atiku, Obi Da Sauran Wadanda Suka Fadi Zabe

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci wadanda basu gamsu da sakamakon zaben 2023 ba a Najeriya da su nemi gyara a kotu
  • A sakon bikin 'Easter', shugaban kasar ya bukace su da su yi hakuri su bari a bi tsarin doka a lamarin
  • Buhari ya yi kira ga yan Najeriya da su yi bikin 'Easter' cikin kauna, tausayi, kyautatawa, juriya, da afuwa yayin da yake taya kowa murna

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci wadanda suke ganin basu gamsu da sakamakon zaben 2023 ba da su nemi kotu ta yi gyara sannan su yi hakuri su bari a bi tsarin doka a lamarin.

A sakonsa na bikin 'Easter' zuwa ga yan Najeriya a ranar Juma'a, 7 ga watan Afrilu, Shugaba Buhari ya kuma karfafawa yan kasar gwiwa kan sabonda muradansu yayin wannan biki da kuma ci gaba da samun karfin gwiwa a kasar suna masu yarda da makoma mai kyau.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Zolayi Gwamnoni Da Suka Sha Kaye A Zaben Sanata, Ya Aika Sako Ga Yan Siyasa

Shugaba Buhari, Atiku Abubakar da Peter Obi
“Ku Tafi Kotu Sannan Ku Jira Hukunci”: Buhari Ga Atiku, Obi Da Sauran Wadanda Suka Fadi Zabe Hoto: Femi Adesina, Mr. Peter Obi, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Buhari ya ce:

"A matsayin kasa, mun bi tsarinb zabe da ya samar da shugabanni na gaba a matakan tarayya da jiha.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na jinjinawa yan Najeriya da suka yarda da tsarin. Yayin da nake taya wadanda aka zaba murna, Na yarda cewa yancin wadanda suke ganin basu gamsu da sakamakon bane su nemi gyara. Ina sa ran za su yi hakuri su jira sannan su bar tsarin doka ta yi aikinta."

Wanda ya zo na biyu da na uku a zaben shugaban kasa na 2023 (Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party) sun riga sun shiga kotu don kalubalantar nasarar zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.

Yan takarar zaben gwamnoni da dama ma suna kalubalantar sakamakon zaben.

Bikin Easter alama ce ta nasarar haske a kan duhu - Buhari

Shugaba Buhari ya jaddada cewa 'Easter' alama ce ta nasarar haske a kan duhu, kuma yana tunatar da mu cewa ko a mawuyacin hali, Allah na da ikon sauya abubuwa su zama alkhairi.

Kara karanta wannan

'Jam'iyyar APC da Mambobin Majalisa Sun Nuna Wanda Suke So Ya Zama Kakakin Majalisar Wakilai'

Ya kuma nuna godiya a kan goyon bayan da ya samu daga yan Najeriya yayin da yake gab da kammala wa'adinsa na shekaru takwas a matsayin shugaban kasa yana mai bayyana shi a matsayin dama mai wuyar samu.

Shugaban kasar ya kuma bukaci yan Najeriya da su yi bikin 'Easter' cikin kauna, tausayi, kyautatawa, juriya, da afuwa.

Ya taya kowa murnar bikin 'Eastar', rahoton The Nation.

Kada ku yi farin ciki tukuna - Primate Ayodele ya yi hasashen tsige wasu zababbun gwamnoni 3

A wani labari na daban, Primate Ayodele, shahararren faston Najeriya ya bukaci zababbun gwamnonin Ogun, Kaduna da na Enugu da kada su yi murna tukuna don ana iya tsige su daga kujerar

Asali: Legit.ng

Online view pixel