Shugaban PDP Na Kasa Ya Sauka Daga Kujerarsa, An Maye Gurbinsa

Shugaban PDP Na Kasa Ya Sauka Daga Kujerarsa, An Maye Gurbinsa

  • Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya sauka daga kujerarsa kamar yadda Kotu ta umarce shi
  • A wata sanarwa da ta fitar, PDP ta maye gurbinsa da mataimakinsa na shiyyar Arewa, Ambasada Iliya Umar Damagun
  • Wannan na zuwa ne awanni bayan Kotu ta umarci Ayu ya daina nuna kansa a matsayin shugaban PDP har sai ta yanke hukunci

Abuja - Shugaban People’s Democratic Party, (PDP) na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya sauka daga kan kujerar shugaban jam'iyya na kasa kamar yadda Kotu ta umarta.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa tuni mataimakin shugaban jam'iyya na arewa, Umar Iliya Damagum, ya maye gurbin Mista Ayu nan take.

Jam'iyyar PDP.
Shugaban PDP Na Kasa Ya Sauka Daga Kujerarsa, An Maye Gurbinsa Hoto: OfficialPDP
Asali: UGC

Damagun zai rike Ofishin Ayu a matsayin muƙaddashin shugaban PDP har zuwa lokacin da Kotu zata yanke hukuncin ƙarshe kan karar da aka shigar gabanta.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Kara Tsanani Bayan Umarnin Kotu, Shugaban PDP Na Ƙasa Ya Shiga Tsaka Mai Wuya

Jam'iyyar PDP ta tabbatar da maye gurbin Ayu da mataimakin shugaban jam'iyya na shiyyar arewa, Damagun, a shafinta na dandalin Tuwita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanarwan da ta wallafa, PDP ta ce:

"Duba da umarnin babbar Kotun Benuwai na haramtawa Iyorchia Ayu bayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyya, mataimakinsa, Ambasada Iliya Umar Damagun, zai maye gurbinsa gabanin Kotu ta yanke hukunci."

Idan baku manta ba, babbar kotu mai zama a Makurɗi, jihar Benuwai, ta hana Ayu nuna kansa a matsayin shugaban PDP har zuwa lokacin da zata yanke hukunci kan shari'ar da zata ci gaba da sauraro ranar 17 ga watan Afrilu.

Mamban jam'iyyar PDP daga jihar Benuwai, Terhide Utaan, wanda ya shigar da ƙarar Ayu da PDP gaban mai shari'a W. I Kpochi, shi ne ya samu wannan umarnin a zaman Kotu.

Da yake jawabi ga 'yan jarida bayan samun umarnin Kotu, mai ƙara ya ce bayan PDP daga gundumar Ayu ta dakatar da shi ranar Lahadi, bai kamata ya ci gaba da zama a Ofis ba.

Kara karanta wannan

"An Hada-Kai da INEC, Za a Murde Zaben Gwamna a Jihar Adamawa" Inji Jam’iyyar PDP

Gwamna Umahi Ya Tona Asirin Ayu, Ya faɗi Yadda Ya Yi wa APC aiki

A wani labarin kuma Gwamnan Umahi Yace Shugaban PDP Na Kasa Tinubu Ya Yi Wa Aiki, Ya Tona Asirin Abinda Ya Faru

Gwamnan Ebonyi na jam'iyyar APC ya ce ba karamar rawa shugaban PDP ya taka ba a nasarar da Bola Ahmed Tinubu ya samu.

A cewar Umahi, ya kamata Tinubu ya saka wa Ayu bisa gudummuwar daya bayar na ƙin sauka daga kujerar shugaban PDP ta ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel