Tsohon Gwamna Ya Yi Wa PDP Raddi Mai Ban Tsoro Bayan Dakatar da Shi Daga Jam’iyya

Tsohon Gwamna Ya Yi Wa PDP Raddi Mai Ban Tsoro Bayan Dakatar da Shi Daga Jam’iyya

  • Ayodele Peter Fayose yana ganin majalisar NWC ta bata lokacinta wajen dakatar da shi daga PDP
  • Tsohon Gwamnan Ekiti ya maidawa Uwar jam’iyya martani ta bakin Lere Olayinka a wani jawabi
  • ‘Dan siyasar ya kyankyasa cewa Iyorcha Ayu yana daf da barin kujerar sa ta shugaban PDP na kasa

Abuja - Ayodele Peter Fayose ya yi watsi da dakatarwar da jam’iyyar PDP tayi masa ta hannun majalisar gudanarwarta na kasa watau NWC.

A rahoton da aka samu daga The Nation, Ayodele Peter Fayose ya yi fatali da wannan mataki da aka dauka, ya ce bai da gindin zama a tsarin mulki.

Tsohon Gwamnan na jihar Ekiti ya ce Dr. Iyorcha Ayu da ‘yan majalisarsa na NWC ba su da hurumi a tsarin mulki da za su iya dakatar da shi.

Kara karanta wannan

Tinubu: Minista Ya Rubutawa DSS Wasika, Ya Nemi a Cafke Peter Obi da Baba Ahmed

A jawabin da ya fitar a ranar Alhamis, ‘dan siyasar kuma jigo a PDP ya dauki lamarin abin dariya.

Lere Olayinka ya fitar da jawabi

Ayo Fayose ya fitar da jawabi na musamman ne ta hannun Mai taimaka masa wajen harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Mista Lere Olayinka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gidan talabijin Channels ya rahoto Lere Olayinka yana cewa dakatarwar shure-shure ce ta PDP da ba zai hana mutuwa ba, yake cewa ba a bi doka ba.

'Yan PDP
Shugabannin PDP a kamfe Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ba a bi dokar kasa ba

Fayose wanda ya yi mulki sau biyu a jihar Ekiti ya ce wannan danyen aiki da uwar jam’iyya tayi ba zai zauna ba domin sam ba a bi dokokin PDP ba.

‘Dan siyasar ya nuna Ayu da ya jagoranci dakatar da ‘ya ‘yan jam’iyyar a makon nan, zai sauka daga kujerar da yake kai ta shugaban PDP na kasa.

Kara karanta wannan

Fayose Ya Yi Zazzafan Martani, Ya Bayyana Wadanda Ke Da Hannu a Matsalolin Najeriya

A jawabinsa, Fayose bai yi bayanin yadda za a bi wajen tunbuke Ayu mai ragowar wa’adi ba.

“Dr. Iyorcha Ayu da mutanensa su na nishadantar da kan su ne kurum da tunanin dakatar da ni a sabon wasan barkwancinsu.
Nan da ‘yan kwanaki, kwanakin Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa zai zo karshe, PDP za ta shiga sabuwar rayuwa.”

- Lere Olayinka.

Kuri'u mafi yawa a 2023

A Jihohin Kano, Bauchi, Filato, Legas, Katsina, an ga ruwan kuri’un Jam’iyyun da suka ci zabe. NNPP ta ta ci kuri’u 1.09 a zaben Gwamnan Kano.

Kun samu labari Jam’iyyar APC ta ba ‘yan takaran PDP ratar raba-ni-da-yaro a zaben Gwamna da aka yi a wasu Jihohi irin Borno, Katsina da Jigawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel