Uba Sani, Umar Bago Da Wasu Zababbun Gwamnoni 3 Da Ke Rike Kujerun Yan Majalisa

Uba Sani, Umar Bago Da Wasu Zababbun Gwamnoni 3 Da Ke Rike Kujerun Yan Majalisa

  • Daga ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, za a samu sabbin fuskoki da za su shugabanci gidajen gwamnatoci daban-daban a kasar
  • Jihohi kamar su Ebonyi, Neja, Zamfara, Sokoto, Taraba, Kano, Filato, Benue, Ribas, Delta, Abia da Enugu za su samu sabbin shugabanni
  • Wasu daga ciki sabbin gwamnonin da aka zaba suna da gogewa a bangaren dokoki wanda za su baje a bangarenb zartarwa

Abuja - Yayin da guguwar zaben gwamnoni ke kara yin kasa, yan Najeriya na zuba ido don ganin abun da sabbin gwamnonin za su yi a jihohinsu mabanbanta.

Mutane da dama na fatan sabbin gwamnonin za su aiwatar da alkawaran da suka dauka yayin yakin neman zabensu.

Zababben gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani
Uba Sani, Umar Bago Da Wasu Zababbun Gwamnoni 3 Da Suka Rike Kujerun Yan Majalisa Hoto: Kaduna state govt.
Source: Facebook

Wasu daga cikin zababbun gwamnonin na da gogewa a bangaren dokoki kasancewar sun rike kujerun yan majalisa. Sune:

1. Rt. Hon. Francis Ogbonna Nwifuru (Ebonyi)

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Kwace Kayan Zabe Sun Kona a Wata Jihar Kudu, Jami'an INEC Sun Tsere

Nwifuru ya kasance gogaggen dan majalisa. Yana zangonsa na biyu a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar Ebonyi.Ana sanya ran zai baje kolin gogewarsa na babban dan majalisar dokoki a matsayin gwamnan jiha.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Sanata Bassey Edet Otu (Cross River)

Sanata Otu ya kasance gogaggen dan siyasa da sanin kan majalisun tarayya guda bibbiyun. Ya wakilci mazabar Calabar Municipality/Odukpani a majalisar tarayya na tsawon shekaru takwas (2003-2011). A 2011, an zabi Otu a matsayin sanata mai wakiltan Cross River ta kudu.

3. Mohammed Umar Bago (Niger)

Hon. Bago mai shekaru 49 shine dan majalisa mai wakiltan mazabar Chanchaga a majalisar wakilai daga jihar Niger. Ya yi suna a matakin kasa ne lokacin da ya yi takarar kakakin majalisar wakilai a 2019 amma ya zo na biyu bayan Femi Gbajabiamika. Dan majalisar ya kasance ma'aikacin banki kafin ya shiga harkokin siyasa.

4. Rt. Hon. Sheriff Oborevwori (Delta)

Rt. Hon. Oborevwori shine kakakin majalisar dokokin jihar Delta mai ci a yanzu. Ya wakilci mazabar Okpe. Dan siyasar mai shekaru 60 ya yi aiki a matsayin kansila a 1996. Oborevwori ya kasance mamba a kungiyoyi daban-daban.

Kara karanta wannan

Hukuncin kyautar da ma'aikatan zabe ke karba wajen wakilan jam'iyyu ranar zabe, Dr Jamil Zarewa

5. Sanata Uba Sani (Kaduna)

Sanata Sani ya kasance injiniya kuma dan siyasa mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a yanzu haka a majalisar dattawa. Kafin ya shiga siyasa, Sanata Sani ya kasance mai fafutukar kare yancin marasa galihu da basu damar samun adalci.

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Zamfara ta sanya dokar hana fita a fadin jihar bayan sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar.

Kamar yadda ta bayyana, ta dauki wannan matakin ne domin hana barkewar rikici a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng