Zaben 2023: Wani Gwamnan Arewa Ya Sake Rasa Kujerar Sanata Ga Jam'iyyar PDP

Zaben 2023: Wani Gwamnan Arewa Ya Sake Rasa Kujerar Sanata Ga Jam'iyyar PDP

  • Sanata Adamu Aliero ya kada gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi don zama sanatan Kebbi ta tsakiya
  • Bagudu ya sha kayi a zaben da aka gudanar cikin kananan hukumomi takwas da ke Kebbi ta tsakiya
  • An samu tsaiko wajen tattara sakamakon zaben biyo bayan bacewar baturen zaben mazabar Mafara a cibiyar tattara sakamakon zabe

Jihar Kebbi - An bayyana Sanata Muhammad Adamu Aliero a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan Kebbi ta tsakiya a zaben yan majalisar dattawa, Daily Trust ta rahoto.

Baturen zabe, Prof. Abbas Yusuf, ya ce sanata Aliero ya samu kuri'a 126,588 inda ya kada Gwamna Abukakar Atiku Bagudu a zaben yan majalisar dattawa.

Bagudu
Aliero Ya Kada Bugudu, Ya Dare Kujerar Sanata. Hoto: Photo: Kebbi State Government
Asali: Facebook

Ya ce Bagudu, wanda kuma shine shugaban kungiyar gwamnoni na jam'iyyar APC ya samu kuri'a 92,389.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Atiku Abubakar Ya Ɗaga Sama, Ya Samu Nasara a Ƙarin Jihohin Arewa 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bagudu ya rasa kujerar sanata

An gudanar da zaben a kananan hukumomi takwas na Gwandu, Bunza, Aliero, Maiyama, Koko-Besse, Jega, Kalgo da Birnin Kebbi wanda su ne suka tada Kebbi ta tsakiya.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta tsayar da tattatara sakamakon zaben sanatan Kebbi ta tsakiya a ranar Lahadi biyo bayan bacewar baturen zaben mazabar Mafara, a Birnin Kebbi.

An bukaci da ya koma ya yi gyare-gyare a wasu alkaluman da ke sakamakon da ya kawo cibiyar tattara sakamakon inda aka neme shi aka rasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel