Zakamakon Zabe: Atiku Ya Samu Nasara a Sakkwato da Kebbi

Zakamakon Zabe: Atiku Ya Samu Nasara a Sakkwato da Kebbi

  • Sakamako na ci gaba da fitowa ta hannun hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a matakin jihohi
  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya kara samun galaba a jihohin arewa guda biyu
  • Ɗan takarar PDP ya samu nasara a jihar Sokoto da Kebbi yayin da Bola Tinubu da Peter Obi ke mara masa baya

Alhaji Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban kasa a inuwar Peoples Democratic Party (PDP) ya samu nasara kan manyan abokan hamayyarsa a jihar Kebbi.

A rahoton The Cable, Baturen zaben INEC, Usman Saidu, ya sanar da cewa Atiku ya lashe kuri'u 285,175 wanda ya ba shi damar zama na ɗaya a sakamakon zaben jihar da aka tattara.

Alhaji Atiku Abubakar.
Atiku Abubakar yana jawabi Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

Babban abokin karawarsa, Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC, ya samu kuri'u 248,088 a matsayin na biyu yayin da Peter Obi na jam'iyyar LP ya tashi da kuri'u 10,682.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: INEC Ta Sanar da Sakamakon Jihar Zamfara, Atiku da Kwankwaso Sun Sha Kashi

Mista Sa'idu ya ƙara da cewa tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP mai kayan daɗi, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zo na huɗu da kuri'u 5,038.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya yi bayanin cewa mutane 1,983,985 ne suka yi rijistar kaɗa kuri'a a jihar Kebbi kuma an tantance 599,201 waɗanda suka fito rumfunan zabe domin sauke nauyi.

Haka zalika ya bayyana cewa mutane 591,475 ne suka jefa ingantattun kuri'u kana an samu kuri'u 31,953 da suka lalace.

Atiku ya cinye zaben jihar Sakkwato

A jihar Sakkwato, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku, ya ƙara samun nasara da kuri'u 288,679.

Kabiru Bala, baturen zaben jihar kuma shugaban jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, shi me ya bayyana sakamakon zaɓen da safiyar ranar Talata.

Bala ya ce Bola Tinubu ya zo na biyu da ƙuri'u 285,444, Peter Obi na uku da kuri'u 6,568, sai kuma Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP wanda ya tashi da kuri'u 1,300.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zabe: Peter Obi da Atiku Sun Sha Kashi Hannun Tinubu, An Faɗi Sakamakon Jihar Benuwai

Bola Tinubu ya cinye Zamfara

A wani labarin kuma INEC Ta Sanar da Sakamakon Jihar Zamfara, Atiku da Kwankwaso Sun Sha Kashi

Tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya samu nasara a zaben shugaban kasan da ya gudana ranar Asabar a jihar Zamfara.

Mai tattara sakamako a jihar ne ya bayyana haka inda ya ce APC ta samu kuri'u mafi rinjaye kana PDP ke biye mata baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel