Wasu Mutane Ke Debe Dukiyar Kasa Suyi Abinda Suka Ga Dama Da Ita

Wasu Mutane Ke Debe Dukiyar Kasa Suyi Abinda Suka Ga Dama Da Ita

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Action Allience ya zargi sauran yan takarar shugaban kasa basu da manufa ga Nigeria
  • Da yawa da ga yan Nigeria basa ji zasu iya taimakawa kasa, shi yasa ake samun wasu matsal-tsalun
  • Dole ne kowa ya shiga taitayinsa, yabi doka da oda in na zaman shugaban kasan Nigeria, dole ne a ji a jiki

Abuja - Tsohon shugaban kula da tsaron shugaban kasa na Nigeria major Hamza Almustapha (mai ritaya) yace akwai tarin ma'adanai da zasu rike Nigeria ba tare da ayi la'akari da man fetir ba.

Almustapha, ya bayyana hakan ne a cikin shirin da Bulama Bukarti lauyan nan da abokan aikinsa, Abba Hikima, da kuma Yan jarida, Nasiru Salisu Zango daga Freedom da Jafar Jafar mamallakin jaridar Daily Nigerian Mai suna Fashin Baki.

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zabe, Tinubu Ya Daukarwa Iyaye Gagarumin Alkawari Da Zai Cika Masu a Kan 'Ya'yansu

Shirin dai na maida hankali ne kan abubuwan da suka shafi al'umma kai tsaye, ana tattaunawa dan samun mafita ko kuma hanyar magance matsalar. A wannan lokacin shirin ya maida hankali ne kan tattaunawa da yan siyasa.

Almustapha
Wasu Mutanene Ke Debe Dukiyar Kasa Suyi Abinda Suka Ga Dama Da Ita Hoto: Premium Times
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wannan makon ranar lahadi 22 ga wannan watan na janairu, shirin ya tattauna da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AA wato Hamza Almustapha.

Hamza Almustapha yace akwai ma'adanai masu yawa

Dan takarar shugaban kasan, kuma tsohon sojan yace akwai ma'adanai kusan 600 da Nigeria ke da shi amma ba ta amfani da shi, alhalin kuma kasuwannnin duniya sunfi sonsa sama da fetir.

Almutsapha na fadin hakan ne bayan da dan jaridar nan Nasiru Salisu ya masa tambaya ko shin wani sinadari na Coladium shine wanda yake nufin zai rike Nigeria?

Kara karanta wannan

'Kana Bukatar Taimako', Martanin Fadar Shugaban Kasa Ga Kalaman Tanko Yakasai Kan Tinubu

Almustapha yace:

"Ba wai iya wannan ba, ko a lokacin tsohon shugaban kasar Libya, Gaddafi yana son amfani da "Uranium" sai yaga ba inda suke dashi da yawa sai Niger, da aka duba sai aka ga har wani bangaren Nigeria ma akwai wannan ma'adanin"
"A yankin arewa maso gabashin Nigeria, akwai tarin ma'adanai da ba'asan iyakar yawansu ba, kuma duka ma'adanan suna da karfi ko kyan da kasuwannin duniya suke bukata.

Tsaro

Jafar Jafar ya tambayi Almustapha sha'anin tsaro, inda yake ce masa hatta shugaba Buhari ma, tsohon soja ne kuma anga yadda ake shan kayi kan matsalar tsaro.

Almustapha ya bada amsa kamar haka:

"Ni ba soja bane kaman shugaba Buhari, watakila shi shigarsa harkar siyasa tasa yayi sauki kuma ya daga kafa, amma ni zan yi duk mai yiwuwa kamar yadda nai bincike kan wannan harkar da kuma wasu hanyoyi dan magance ta"

Kara karanta wannan

Rigima Ta Kunno a Ralin Peter Obi Na Jihar Kano, Dan Takarar Gwamnan Da Shugabannin LP Sun Kauracewa Taron

Almustapha yace ya fito a wannan jam'iyyar ta AA dan manufofinta guda shida da suka hada ci gaba da tattalin arziki da sauransu ya saje da manufofi irin nasa.

Zaka iya kallon bidiyon tattaunawar anan

Asali: Legit.ng

Online view pixel