2023: ‘Ya’yanku Za Su Ci Abinci Su Koshi Idan Na Zama Shugaban Kasa, Tinubu Ga Iyaye

2023: ‘Ya’yanku Za Su Ci Abinci Su Koshi Idan Na Zama Shugaban Kasa, Tinubu Ga Iyaye

  • Yan kwanaki kafin babban zaben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya daukarwa iyaye babban alkawari
  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya ce da zaran ya zama shugaban kasa, babu dan da zai sake bacci da yunwa a kasar nan
  • Tinubu ya ce abinci zai yawaita a Najeriya kuma talaka zai samu damar kula da lafiyarsa da ilimi cikin sauki

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya ba iyaye tabbacin cewa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023, abinci zai yawaita a kasar don ciyar da 'ya'yansu.

Tinubu ya bayar da tabbacin ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Janairu, a Abuja a wajen wani taro da jaridar Daily Trust ta shirya mai taken "yin tambayoyi kan ajandar shugabancin kasa na 2023."

Kara karanta wannan

Tinubu Na Da Tunani Irin Na Sarakunan Kama Karya, Naja'atu Ta Tono Bakin Shafin Dan Takarar APC

Bola Tinubu
2023: ‘Ya’yanku Za Su Ci Abinci Su Koshi Idan Na Zama Shugaban Kasa, Tinubu Ga Iyaye Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Zan inganta kiwon lafiya, ilimi da tsaro idan na zama shugaban kasa, Tinubu

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya kuma ba al'ummar tabbacin inganta bangarorin kiwon lafiya, ilimi da gidaje ta yadda talaka zai iya mallakarsu ba tare da fargaba ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma jaddada aniyarsu na son karfafa tsarin tsaro a kasar domin kawar da kalubalen da tsaron kasar ke fuskanta kama daga sace-sacen mutane, fashi da makami da sauransu.

Jaridar ta nakalto Tinubu yana cewa:

"Muna so Najeriya ta zama kasa da babu iyayen da za su tura 'ya'yansu bacci da yunwa, suna tunanin ya gobe za ta kasance za a samu abinci kuwa. Muna ba ku tabbacin cewa abinci zai wadata don ku ciyar da 'ya'yanku.
"Za mu saukaka bangaren kiwon lafiya, ilimi da gidaje ta yadda kowa zai iya mallakarsu, kuma abu mai muhimmanci, za mu jagoranta sannan mu samar da tsauraran matakan tsaro wanda zai karfafa tsarin tsaro a kasar da kawo karshen sace-sacen mutane, fashi da makami da kuma rikice-rikicen daga kasarmu."

Kara karanta wannan

'Kana Bukatar Taimako', Martanin Fadar Shugaban Kasa Ga Kalaman Tanko Yakasai Kan Tinubu

Tinubu bai damu da Najeriya ba, kansa kawai ya sani, Naja'atu Muhammad

A wani labarin kuma, tsohuwar hadimar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Naja'atu Muhammad ta yi ikirarin cewa Bola Tinubu ba zai iya mulkin Najeriya ba.

Naja'atu wacce ta fice daga jam'iyya mai mulki, ta ce Tinubu kansa kawai ya sani, cewa ba Najeriya bace a gabansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel