Gwamnan PDP Ya Tona Abin da Tsohon Gwamnan APC Ya yi da Zai Bar Mulki
- Gwamna Ademola Adeleke ya yi wa Sarakunan Osun bayanin bashin da ake bin Gwamnatin jihar
- Mai girma Gwamnan ya ce Gwamna Gboyega Oyetola ya karbo bashin N18bn a karshen wa’adinsa
- Ana bin Jihar Osun bashin Naira Biliyan 407, kuma babu kudin da tsohon Gwamna ya bari a asusu
Osun - Mai girma Gwamnan Osun, Ademola Adeleke ya ce ana bin Gwamnatin jihar bashin abin da ya kai Naira Biliyan 407.32 a halin yanzu.
A rahoton da aka fitar a gidan talabijin na Channels TV, an fahimci cewa daga cikin bashin da ake bin jihar, har da N76bn na albashi da fansho.
Gwamna Ademola Adeleke ya ce Gboyega Oyetola wanda ya bar karagar mulki ya karbo bashin N18.04bn bayan ya rasa zaben tazarce a Yuli.
Adeleke ya fadawa jama’a babu wani karin bayani a kan lokacin da Gwamnatin Osun za ta biya bashin da ta karba a hannun gwamnati da bankuna.
Gwamnan ya fasa-kwan ne lokacin da yake jawabi da ya hadu da masu rike da sarautar gargajiya a babban birnin Osogbo a yammacin Alhamis.
Har zuwa yanzu, Gwamna Adeleke ya ce ba a san bashin nawa ‘yan kwangila suke bin jihar ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Na iske bashi iri-iri - Adeleke
The Cable ta rahoto Mai girma gwamna yana cewa akwai kunshi takwas na bashi iri-iri da ya gada daga hannun gwamnatin Adeleke da ya tafi.
Bashin da gwamnatin Osun za ta biya sun hada da na cikon albashi, gibin kasafin kudi, bashin bankin ‘yan kasuwa, da rarar arzikin man fetur.
Sannan Ademola Adeleke ya ce akwai bashi daga kasashen ketare, bashin gina abubuwan more rayuwa daga CBN da tallafin gwamnatin tarayya.
Akwai sauran aiki
Wa’adin wadannan bashi da aka karba ya fara ne daga tsawon watanni 16 zuwa shekaru 28.
A lokacin da ya karbi mulki a ranar 29 ga Nuwamba, Gwamnan Osun ya ce abin da ya samu a asusun jihar kudin da za a biya albashin watan ne kurum.
Oyetola zai fadi dalilin da ake bin bashin fansho duk ya karbo aron N50bn, kuma bankuna su fadi dalilin bada aron da wa’adinsa ya wuce shekaru hudu.
AGF: An gano N30bn - EFCC
Rahoton da ak asamu shi ne daga cikin N109bn da ake zargin Idris Ahmed ya handame a ofishin AGF, Shugaban EFCC ya ce sun iya gano N30bn.
Abdulrasheed Bawa yace daga Junairu zuwa Disamban nan, sun gano N134,33,759,574.25, baya ga kudin kasar waje da aka iya karbewa.
Asali: Legit.ng