Manyan Arewa Sun Koka da Tinubu Kan Shirin Kafa Sansanin Sojin Amurka da Faransa

Manyan Arewa Sun Koka da Tinubu Kan Shirin Kafa Sansanin Sojin Amurka da Faransa

  • Manyan Arewa sun aika da gargadi ga shugaba Bola Tinubu kan yunkurin kafa sansanin Amurka da Faransa a Najeriya
  • Sun tura gargadin ne cikin wata budaddiyar wasika tare da bayyana irin hadarin da ke cikin amincewa da kafa sansanin
  • Sojojin kasashen Faransa da Amurka suna yunkurin dawowa Najeriya ne bayan an kore su daga wasu yankunan Afrika

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Yunkurin Kasashen Faransa da Amurka domin sauya sansanin sojojinsu daga yankin Sahel zuwa tarayyar Najeriya ya fara samun korafi.

Shugaba Tinubu
Manyan Arewa sun ce kafa sansanin sojan Amurka da Faransa a Najeriya babban kuskure ne. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Korafin ya fara ne yayin da wasu manyan Arewa suka yi kira na musamman ga shugaban kasa Bola Tinubu kan nuna kin amincewarsu da kudirin.

Kara karanta wannan

Gwamnati na shirin kawo hanyar da za ayi sallama da matsalar lantarki

Manyan Arewa sun rubutawa Tinubu korafi

Dattawan sun yi kiran ne cikin wada budaddiyar wasika da suka aike ga shugaban kasa da shugabannin majlisar dokokin Najeriya suna cewa lalle bai kamata ƙasar ta amince da kudirin ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar jaridar Daily Trust, wadanda suka sa hannu a wasikar sun hada da Farfesa Abubakar Siddique, Farfesa Kabiru Sulaiman Chafe da Farfesa Attahiru Jega.

Har ila yau fitattun mutanen sun hada da Farfesa Jibril Ibrahim, Auwal Musa (Rafsanjani) da kuma Y.Z Ya'u.

Wasikar ta yi nuni da cewa kasashen Amurka da Faransa suna yunkurin saka Najeriya cikin yarjejeniyar da za ta basu damar kafa sansanin soja a Najeriya bayan korarsu da aka yi a Mali, Burkina Faso da kasar Nijar.

Takardar ta kuma kara da cewa ba a cimma manufar yaki da ta'addanci da ta sa aka kafa sansanin a Nijar ba, saboda haka ko an kawo su Najeriya ma bata lokaci ne.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sandan Kano suka yi wawason 'yan daba sama da 3000 a shekara 1

Illar da kafa sansanin sojoji zai haifar

Manyan na Arewa sun kara da cewa kawo sojojin kasashen waje Najeriya ba abin da zai haifar sai asara da ɗan da na sani.

Sun yi nuni da cewa kafa sansanin soja a Nijar ba abin da ya kara sai yawaitar 'yan ta'adda da ayyukan ta'addanci a kasar.

Har ila yau sun fada wa shugaban kasan cewa kafa sansanin zai kawo tashin farashin kayayyaki wanda hakan zai yi tasiri cikin rayuwar mazauna wuraren.

Cikin illolin da ake gujewa sun hada da lalata muhalli da zaman nasu zai kawo a yankin da aka kafa su, cewar jaridar the Cable

Amma har yanzu ba a samu martani daga fadar shugaban kasa ko majalisun kasar a kan wasikar wadannan manya da masana ba.

Nijar da Faransa sun samu sabani

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Faransa ta yi watsi da umarnin sojin Nijar na fatattakar jakadanta a jamhuriyar dake cikin rikicin juyin mulki

Sojojin Nijar sun ba jakadan Faransa sa'o'i 48 a kan ya tattara kwamutsansa ya fice daga kasar amma an cigaba da kai ruwa rana tsakanin ƙasashen biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel