Labari mai zafi: Tsageru Sun Kona Babban Ofishin Kamfen PDP a Jihar Gombe

Labari mai zafi: Tsageru Sun Kona Babban Ofishin Kamfen PDP a Jihar Gombe

  • An wayi gari da ganin wuta tana kamawa a ofishin yakin neman zaben jam’iyyar PDP a jihar Gombe
  • Kwamitin yakin neman zaben Alhaji Mohammed Barde yace jam’iyyar APC ta sa aka yi wannan aiki
  • Jami’in ‘yan sanda sun tabbatar da cewa an sa wuta a ofishin na PDP, kuma ana bincike kan lamarin

Gombe - Maganar da ake yi, ofishin yakin neman zaben Gwamna a jam’iyyar hamayya ta PDP a jihar Gombe yana ci da wuta.

A rahoton da muka samu daga Daily Trust, an wuta yana kona ofishin takarar Gwamnan Alhaji Mohammed Barde a Jam’iyyar PDP.

Haka zalika wasu ofisoshin da ke kusa da bangaren sauke shugaban kasa a cikin gidan gwamnatin jihar Gombe sun kama da wuta.

Zuwa yanzu ba a ji ainihin abin da ya jawo wannan gobara ba, amma PDP tana zargin danye aikin 'ya 'yan jam’iyyar APC mai mulki ne.

Kara karanta wannan

2023: Daraktan Yakin Neman Zaben Atiku Ya Gana da Gwamnan Tsagin Wike, Bayanai Sun Fito

Aikin APC ne - Kwamitin kamfen PDP

A wani jawabi da ya fito daga bakin Junaidu Usman Abubakar, jam’iyyar PDP ta tabbatar da cewa ta gamu da asara a dalilin gobarar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Junaidu Usman Abubakar shi ne Mataimakin Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben Atiku/Dan Barde 2023 a Gombe.

Atiku a Gombe
Kamfen PDP Jihar Gombe Hoto: Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Jawabin kwamitin Atiku/Dan Barde

"A safiyar yau ‘yan bangar siyasa da ake zargin yaran APC ne sun kai hari a ginin da kwamitin yakin neman zaben Jibril Barde yake amfani da shi wajen kamfe, sun kona ginin, sannan suka lalata dukiyoyi.
Harin nanda aka kai a tsorace wanda ba shi ne na farko a watannin nan ba, ya tabbatar da matsayar gwamnati na rikici da ta’adi, hakan barazana ce ga zaman lafiyar jihar da ya kamata kowa yayi tir da shi.
Sau da yawa ‘Dan takaran Gwamnan jihar Gombe a PDP, Alh Muhammad Jibrin Barde yana Allah wadai da siyasar daba da banga, yana goyon bayan a zauna da matasan Gombe ta hanyoyi masu ma’ana.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Rasa Jiga-Jigan Yakin Neman Zabensa A Yankin Arewa Maso Gabas

Ana kira ga mutanen kwaran jihar Gombe suyi gaggawan watsi da wannan kama-karya a lokacin zaben 2023. Manufar Barde ita ce kare rai da dukiya, ya ba mata da matasa dama, ya kawo cigaba.

Ana sauraron Gwamnati

Jami’in gwamnatin jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli, yace za iyi magana a game da lamarin.

Da jaridar ta tuntubi Kakakin ‘yan sanda, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya tabbatar da harin, yace za an fara bincike domin a kama masu laifi.

Hadarin Bayo Onanuga

Dazu an ji Bayo Onanuga ya bada labari yana kan titi a Abuja, ya ci karo da tawagar motocin Atiku Abubakar, aka yi rashin dace wata mota ta duro masa

Kamar yadda ya fada a shafin Facebook, direban da ya buge shi ya tsere, ko da ya bi motar, ba ta tsaya ko ina ba sai wani gidan Atiku Abubakar a Asokoro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng