2023: Atiku Ya Bayyana Hanya Ɗaya da 'Yan Najeriya Zasu Hukunta Jam'iyyar APC

2023: Atiku Ya Bayyana Hanya Ɗaya da 'Yan Najeriya Zasu Hukunta Jam'iyyar APC

  • Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga yan Najeriya su hukunta APC a zaben 2023
  • Atiku yace mutane ke da wuka da nama a hannunsu, su hana APC kuri'unsu don kawar da ita da ceto ƙasar nan daga rushe wa
  • Tsohon mataimakin shugaban kasan na ɗaya daga cikin waɗanda ake ganin zasu iya karban Najeriya a zabe mai zuwa

Abuja - Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya bukaci 'yan Najeriya su hukunta jam'iyyar APC ya hanyar hanata kuri'unsu a 2023.

Atiku ya yi wannan kira ne a wani sakon Email da ya tura wa magoya bayansa ranar Lahadi 4 ga watan Disamba, 2022, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Atiku Abubakar.
2023: Atiku Ya Bayyana Hanya Ɗaya da 'Yan Najeriya Zasu Hukunta Jam'iyyar APC Hoto: Atiku Abubakar/facebook
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa matukar ana fatan Najeriya ta gyaru, ya zama wajibi a haɗa kai kuma a ja kowa a jiki kuma matuƙar ana son ƙasa ta dunkule dole a samu shugabanci nagari da zai tunkari waɗannan muhimman abubuwan.

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Ja Wa Kansa, Wani Babban Jigon APC Ya Fice Daga Jam'iyyar

Ɗan takarar PDP yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Zabe mai zuwa a ƙasar nan aikin ceto ne da kokarin tseratar da rayuwar Najeriya. APC mai mulki ta mayar da mu baya kuma mun yi nisa daga turbar haɗin kai da aminci."
"Shiyasa ni da kai ya zama hakki a kanmu mu yi aiki tare don ceto ƙasar mu kuma wannan aikin ceton zai fara ne daga hana APC kuri'un mu a 2023. Sun gaza mafi munin gazawa dole mu hukunta su."
"Kawar da APC kaɗai bai isa ba, sai mun cure wuri ɗaya a PDP, jam'iyya ɗaya tilo dake da karfin yin ƙasa-ƙasa da APC. Idan ka dangwalawa PDP ka zaɓi jam'iyyar dake da tarihin haɗa kan ƙasa da aminci."

Atiku ya ƙara da jan hankalin kowanensu ya kara zage dantse wajen jawo 'yan uwa, iyalai da abokanan ariziki waɗanda zasu ba da gudummuwa wurin tabbatar da nasarar PDP.

Kara karanta wannan

2023: Dubbannin Mambobin Jam'iyyun PDP da LP Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Arewa

Jiga-Jigan PDP Sun Gana da Obasanjo a Ogun

A wani labarin kuma Mataimakin Atiku, Tambuwal, Da Wasu Jiga-Jigan PDP Sun Lallaba Sun Gana da Obasanjo

A ci gaba da faɗi tashin ganin an lalubo hanyar maslaha a PDP, tsohon shugaban ƙasa, Obasanjo ya karbi bakuncin manyan kusoshin jam'iyyar PDP na ƙasa.

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya shata layi inda ya kafa sharaɗin tunbuke shugaban PDP na ƙasa matsayin hanya ɗaya tilo na dawowar zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262