Ba Zan Zauna Gidan da Aka Lullube da Karya Ba, Jigon APC Ya Fice Daga Jam'iyyar

Ba Zan Zauna Gidan da Aka Lullube da Karya Ba, Jigon APC Ya Fice Daga Jam'iyyar

  • Jigon jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kuros Riba, Ray Murphy, ya fice daga jam'iyyar, yace ba zai zauna cikin makaryata ba
  • Yace Najeriya na bukatar nagartaccen shugaban wanda ya zarce barkwanci subutar baki da APC ke kokarin kakabawa
  • A 'yan makonnin nan, Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC ya saki baki a wuraren kamfe daban-daban

Cross River - Wani babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kuros Riba, Ray Murphy, ya fice daga jam'iyyar.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Murphy, tsohon mashawarcin John Oyegun, tsohon shugaban APC na ƙasa, yace 'yan Najeriya na bukatar abinda ya zarce, "Barkwancin subutar harshe," wanda ke cin kasuwa a APC.

Ray Murphy.
Sanatan Arewa Ya Tsallake Rijiya Da Baya Yayin da Yan Bindiga Suka So Kashe Shi Hoto: thecable
Asali: UGC

Jaridar The Cable ta rahoto cewa a makonnin da suka shige, Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, ya yi wasu ɓaranɓarama a gaban jama'a lamarin da ya haddasa cece-kuce a tsakanin 'yan ƙasa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Abokin Takarar Peter Obi Ya Yi Garumin Zargi A Kan Tinubu

Murphy ya bayyana cewa 'yan Najeriya sun tsinci kansu cikin matsanancin yanayi kuma a halin yanzu suna bukatar abinda ya zarce tanadin jam'iyya mai mulki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yace:

"Ba zan yi nadama ba, na rasa abokai da yawa saboda suna zaton zan cigaba da rayuwa cikin yaudara, a tunaninsu zan zama irinsu, na yi Allah wadai da mulkin APC a sirrance kuma na yaba wa mata a bainar jama'a."
"Ban san yadda zan maida harshena mai wasan barkwanci ba. Ko kaɗan bana dana sanin barin APC inda na ba da gagarumar gudummuwa a kokarin kafa kyakkyawar gwamnati mai kyau."
"Ba zan goyi bayan tikitin takarar da ya saɓa wa al'adar banbance banbancen da muke da su a ƙasarmu ba."

Najeriya na bukatar abinda ya zarce APC - Murphy

Mista Ray Nurphay ya ƙara da cewa a halin da mutane suka wayi gari yanzu, Najeriyama bata bukatar yan wasan barkwanci masu ɓaranbarama a gaban jama'a.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Arewa Ya Lallaba Patakwal, Ya Sa Labule da Wike

Punch ta rahoto ya cigaba da cewa:

"Na yi imani Najeriya na bukatar nagarta, tana bukatar abun da ya zarce wasan barkwanci da subutar harshe wanda jam'iyyar APC ke kokarin tallata wa al'umma don ta ƙara gurɓata abubuwa."
"Ban yi nadama ba saboda ni mai son gaskiya ne da kuma kokarin yin dai-dai. Wannan ne aikin mu kuma kome zafin rana muna tsaye kan gaskiya, zamu raba gari da duk wanda ya zaɓi ƙarya."

A wani labarin kuma Mataimakin Atiku, Tambuwal, Da Wasu Jiga-Jigan PDP Sun Lallaba Sun Gana da Obasanjo

A ci gaba da faɗi tashin ganin an lalubo hanyar maslaha a PDP, tsohon shugaban ƙasa, Obasanjo ya karbi bakuncin manyan kusoshin jam'iyyar PDP na ƙasa.

Duk da babu cikakken bayani kan abinda suna fi maida hanhakali a zaman nasu na sirri, ana hasashen yanada alaƙa da rashin zaman lafiya da ya haddasa Wike ya kafa tafiyar G5 a PDP.

Kara karanta wannan

2023: Dubbannin Mambobin Jam'iyyun PDP da LP Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Arewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel