Kada Ka Manta Da Jihar Ribas Idan Ka Zama Shugaban Kasa, Wike ga Kwankwaso

Kada Ka Manta Da Jihar Ribas Idan Ka Zama Shugaban Kasa, Wike ga Kwankwaso

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya gabatar da wani babban bukata da yake so Rabiu Kwankwaso ya cika masa a 2023
  • Wike ya roki dan takarar shugaban kasa na NNPP da ya tuna da mutanen jiharsa ta Ribas idan ya yi nasara a babban zabe mai zuwa
  • Jagoran kungiyar 'Integrity Group' na PDP ya sha alwashin taimaka da aljihunsa don yiwa tsohon gwamnan na jihar Kano kamfen a Ribas

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya roki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Kwankwaso, da ya tuna da mutanen jihar Ribas idan ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Wike ya fadi hakan ne a ranar Litinin, 21 ga watan Nuwamba, a bikin bude hanyoyi Mgbutanwo da ke karamar hukumar Emohua da ke jihar, yayin da ya gayyaci dan takarar shugaban kasar don kaddamar da aikin, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wike da Sauran Gwamnonin G-5 Sun Kafa Sabuwar Kungiya, Sun Ce Sam Ba Zasu Taya Atiku Kamfen Ba

Wike da Kwankwaso
Kada Ka Manta Da Jihar Ribas Idan Ka Zama Shugaban Kasa, Wike ga Kwankwaso Hoto: Punch
Asali: UGC

Kwankwaso babban kadara ne ga PDP musamman a jihar Kano amma aka bari ya fice

Wike wanda ya bayyana Kwankwaso a matsayin aboki kuma dan uwa ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasar na nufin Najeriya da alkhairi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewar shi da gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wanda ake yiwa lakabi da G-5 zasu ci gaba da goyon abun da yake shine daidai wanda zai kuma taimaki kasar nan.

“Don haka idan kayi nasara ka tuna da mu, ka tuna da mu a jihar Ribas,” cewar Wike.

Wike ya kara da cewar yana daya daga cikin yan tsirarun mutanen da suka hadu da Kwankwaso, wanda ya kasance tsohon dan PDP, da kada ya bar jam’iyyar saboda ya san cewa shi din kadara ce babba ga PDP, musamman a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Ayu Barawo Ne, Ya Fara Gina Jami'a a Jihar Benue: Nyesom Wike

Ya kara da cewa:

“Na tuna lokacin da naje ganawa da kai a gidanka da ke Abuja don rokonka a kan kada kabar jam’iyyar PDP saboda na san kai kadara ce ga jam’iyyar. Harma lokacin da suka fada mani cewa na kyale ka, na ki.”

Zan taimaka da kudi don yi maka kamfen a Ribas, Wike ga Kwankwaso

Wike ya jaddada cewar tsohon gwamnan na jihar Kano na da abun bukata don saita Najeriya, yana mai cewa abun bakin ciki ne cewa yanzu ba a jam'iyya daya suke ba.

Ya kuma dauki alkawarin bayar da gudunmawar kayayyaki don kamfen din Kwankwaso a Ribas, rahoton Channels TV.

Asali: Legit.ng

Online view pixel