Dan a Mutun Tsohon Gwamna Ya Yi Murabus, Ya Ajiye Kujerarsa a Gwamnatin PDP

Dan a Mutun Tsohon Gwamna Ya Yi Murabus, Ya Ajiye Kujerarsa a Gwamnatin PDP

  • Farfesa Zacchacus Adangor, kwamishinan shari'a kuma Antoni Janar na Ribas ya ajiye aiki daga mukarraban Gwamna Similanayi Fubara
  • An gano cewa Farfesa Adangor ya yi murabus ne bayan da aka dauke shi daga ma'aikatar shari'a zuwa ta ayyuka na musamman
  • Farfesa Adangor ya ce ya hakura da yi wa gwamnatin Fubara aiki yana mai zargin gwamnan da yi masa katsalandan a ayyukansa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Ribas - Kwamishinan shari'a kuma Antoni Janar na jihar Ribas, Farfesa Zacchacus Adangor ya yi murabus daga gwamnatin Similanayi Fubara.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Farfesa Zacchacus Adangor ya yi murabus ne bayan da ya ki karbar sabon canjin wajen aiki da aka yi masa zuwa ma'aikatar ayyuka na musamman.

Kara karanta wannan

Gwamna ya rage kudin makaranta yayin da ya ƙara albashin malamai, zai ba dalibai aiki

Kwamishinan shari'a jihar Ribas, Farfesa Zacchacus Adangor ya yi murabus
Kwamishinan Ribas mai biyayya ga Wike ya yi murabus. Hoto: @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

Gwamnatin Ribas ta yi sauye-sauye

An ruwaito cewa Gwamna Fubara ya canja wa Farfesa Adangor wanda ɗan a mutun Nysome Wike ne wajen aiki tare da wani Isaac Kamalu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamalu wanda shi ma na hannun daman Wike ne an dauke shi daga kwamishinan Kudi zuwa kwamishinan samar da ayyuka da tattalin arziki.

Gwamnatin jihar ta umarci mutanen biyu da su gaggauta mika mulkin ma'aikatunsu zuwa ga sakatarorin din-din nan na ma'aikatun, rahoton jaridar Premium Times.

Kwamishinan shari'a ya yi murabus

Sai dai rashin gamsuwa da wannan canji, Farfesa Adangor ya aika wasikar murabus dinsa ga sakataren gwamnatin jihar, Dr. Tammy Danagogo a ranar 24 ga watan Afrilu.

Farfesa Adangor a cikin wasikar ya ce ya hakura da yi wa gwamnatin Fubara aiki yana mai zargin gwamnan da yi masa katsalandan a ayyukansa.

Kara karanta wannan

"Allah kaɗai ke ba da mulki," Atiku ya mayar da martani kan zargin cin amana a taron NEC

Sanarwar ta ce:

"Ina so in sanar da kai cewa na gaji da yi wa gwamnatin Similanayi Fubara aiki. A matsayina na kwamishinan shari'a, gwamnan jihar yana katsalandan a ayyukana.
"Duk da na kwashe shekara biyar ina yi wa gwamnatin jihar Ribas aiki, amma yanzu an kai ni bango ba zan iya ci gaba da yin aikin ba."

'Yan majasa sun bijirewa Fubara

A wani labarin daga jihar Ribas, Legit Hausa ta ruwaito cewa 'yan majalisar jihar Ribas sun nuna wa Gwamna Similanayi Fubara karfin ikonsu kan abin da ya shafi dokar kananan hukumomin jihar.

An ruwaito 'yan majalisar sun amince da kudurin yin gyara ga dokar kananan hukumomin jihar tare da rattaba hannu ta zama doka ba tare da amincewar gwamnan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel