Majalisar Dokokin Jihar Ekiti Ta Yi Sabon Kakakin Majalisa Bayan Mutuwar Tsohon

Majalisar Dokokin Jihar Ekiti Ta Yi Sabon Kakakin Majalisa Bayan Mutuwar Tsohon

  • Majalisar dokokin jihar Ekiti ta naɗa sabon shugabanta biyo bayan rasuwar tsohon kakaki a watan Oktoba, 2022
  • A zaman yau Talata, mambobin majalisar sun zaɓi Gboyega Aribisogan, a matsayin sabon jagoransu
  • Bayan rantsar da shi a matsayin kakaki, ɗan majalisar ya yi alkawarin sauke nauyin da aka ɗora masa iyakar karfinsa

Ekiti - Mambobin majalisar dokokin jihar Ekiti sun zaɓi tsohon jagoran harkokin kasuwancin gwamnati, Gboyega Aribisogan, a matsayin sabon kakakin majalisar.

Magatakardan majalisar, Mista Tola Esan ne ya rantsar da sabon Kakakin a zaman yan majalisun na yau Talata, 15 ga watan Nuwamba, 2022.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Aribisogan ya fito ne daga yankin Ijesha-Isu da ke ƙaramar hukumar Ikole a jihar Ekiti, kudu maso yammacin Najeriya.

Kakakin majalisar dokokin Ekiti, Aribisogan.
Majalisar Dokokin Jihar Ekiti Ta Yi Sabon Kakakin Majalisa Bayan Mutuwar Tsohon Hoto: punchng
Asali: UGC

Kujera lamba ɗaya a majalisar ta zama babu kowa ne biyo bayan mutuwar tsohon kakaki, Funminiyi Afuye, bayan zuciyarsa ta buga a makonnin da suka wuce.

Kara karanta wannan

2023: 'Komai Ya Zo Karshe' Bukola Saraki Ya Magantu Kan Sasanta Atiku da Wike a PDP

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Honorabul Afuye, mai wakiltar mazaɓar Ikere ta I a majalisar dokokin ya rasune ranar 19 ga watan Nuwamba, 2022 a Asibitin koyarwa na jami'ar jihar Eikiti (EKSUTH).

Bayanai sun nuna cewa an yi Jana'izarsa ranar Jumu'a ta makon da ya gabata a gidansa da ke Ikere-Ekiti.

Yadda aka zabi sabon kakakin majalisar

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Aribisogan, mamba a majlisar na tsawon zango biyu, ya samu nasarar zama kakaki ne a bayan samun kuri'u 15, inda ya lallasa Olubunmi Adelugba mai wakiltar mazaɓar Emure, mai kuri'a 10.

A zaman, Tajudeen Akingbolu (Ekiti West 1) ya zaɓi Aribisogan kuma ya samu goyon bayan Adegoke Olajide na mazaɓar Efon, yayin da Bode Oyekola (Ekiti West 2) ya nuna Olubunmi Adelugba.

Da yaƙe tsokaci bayan rantsar da shi, Sabon kakakin majalisar ya gode wa abokanan aikinsa bisa wannan yarda da suka nuna kansa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Halaka Matar Shugaban Ƙaramar Hukuma a Jihar Arewa

Aribisogan yace, "Zan yi kokarin sauke nauyin da aka ɗora mun bakin gwargwadon karfina kuma zan kare martabar kundin mulkin ƙasa da dokokin majalisa."

A wani labarin kuma Sanata Bukola Saraki Yace nan ba da daɗewa ba yan Najeriya zasu sha mamaki game da rikitin Atiku da Wike

Da yake hira da yan jarida a wurin addu'ar cikar mahaifinsa shekara 10 da rasuwa, Saraki yace rigingimun da PDP ke fama da su na gab da zama tarihi.

Yace jam'iyyar PDP zata haɗa kai ta dunƙuƙe wuri guda domin kwace mulki hannun APC a 2023 domin babban burin yan Najeriya kenan a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel