APC Ta Na Neman Kuri’u Miliyan 5 a Legas Domin Tinubu Ya Yi wa Atiku, Obi Fintinkau

APC Ta Na Neman Kuri’u Miliyan 5 a Legas Domin Tinubu Ya Yi wa Atiku, Obi Fintinkau

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi zama da shugabannin APC na Legas a sakariyar jam’iyya da ke jihar
  • Jam’iyyar APC ta reshen Legas za tayi kokari wajen ganin Bola Ahmed Tinubu ya samu kuri’u miliyan 5
  • An yi zaman ne da su Gwamna Babajide Sanwo-Olu da Shugaban majalisar Legas, Mudasiru Obasa

Lagos - Jam’iyyar APC ta reshen jihar Legas, tayi alkawarin kawowa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kuri’u miliyan biyar a zaben shugaban kasa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto APC ta Legas tana mai wannan alwashin a lokacin da Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ziyarci sakatariyar Jam’iyyar.

Babajide Sanwo-Olu ya zauna da sauran shugabannin APC na reshen Legas, inda yi alkawari da bakinsa cewa za su ba Bola Tinubu babbar nasara.

Sanwo-Olu yace lokaci ya yi da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na jiharsa za suyi wa Tinubu mai neman zama shugaban kasa sakayyar alheran da ya yi masu.

Kara karanta wannan

2023: Lokaci Ya Yi Da Yan Arewa Zasu Saka Wa Tinubu Bisa Alherin da Ya Musu a Baya, Shettima

Gwamnan yace ‘dan takaran shugaban kasar ya taimakawa ‘yan jam’iyyarsa ta APC musamman sa’ilin da ya rike kujerar Gwamna daga 1999 zuwa 2007.

Shugaban APC a Legas ya yi kira

Shugaban APC na Legas, Fasto Cornelius Ojelabi ya yi kira ga ‘yan jam’iyya su tabbatar Bola Tinubu ya tashi da akalla kuri’u miliyan biyar a badi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bola Tinubu
Bola Tinubu wajen gabatar da manufofinsa: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

“Muna da masu yin zabe mutum miliyan bakwai a jihar nan, muna nemawa jagororinmu akalla kuri’u miliyan biyar.

- Fasto Cornelius Ojelabi

Da yake maganar shugabanninsu, Legit.ng Hausa ta fahimci Cornelius Ojelabi yana nuni ne ga tsohon Gwamna Bola Tinubu da irinsu Babajide Sanwo-Olu.

Obasa yana so Legas ta bada tazara

A na sa jawabin, Rt. Hon. Mudasiru Obasa ya tabbatar da APC tana neman gagarumar nasara a kan ‘yan adawa a zaben da za ayi a farkon shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

APC da Tinubu Na Shirin Ba Atiku Mamaki a Adamawa, Za a Tika Shi da Kasa a Mahaifa

Obasa shi ne shugaban majalisar dokokin Legas, kuma babban masoyin Bola Tinubu.

Shi kuwa da ya tashi magana a taron, Bola Tinubu ya nemi ‘yan APC su ajiye sabaninsu a gefe, su hada-kai domin ganin ya yi nasara a babban zaben.

Atiku ya yi kasuwa

A jihar Oyo, kun samu labari Mayoress Olubukola Olayinka tace babu ita babu jam’iyyar Labour Party ta su Peter Obi, ta kawo dalilinta na canza sheka.

‘Yar siyasar da magoya bayanta za su dage domin ganin Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa sun doke APC, LP da NNPP a zaben shugabancin kasa da za ayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel