Tinubu Ya Sake Barin Najeriya, Masoyan ‘Dan Takara Sun Fito da Shirin da Suke yi

Tinubu Ya Sake Barin Najeriya, Masoyan ‘Dan Takara Sun Fito da Shirin da Suke yi

  • Asiwaju Bola Tinubu da Kashim Shettima sun tafi kasar Ingila da nufin su huta kafin a fara kamfe gada-gadan
  • A lokacin da jirgin Bola Tinubu ya bar Najeriya, shi kuma Atiku Abubakar mai takara a PDP yake dawowa
  • Sai a watan Oktoba ‘dan takaran na APC zai dawo domin fara kamfe, kafin nan masoya za su fara yin tattaki

Abuja - Masu takarar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a APC, Asiwaju Bola Tinubu da Sanata Kashim Shettima sun bar Najeriya.

Punch ta fahimci cewa a ranar Asabar, ‘yan takaran na jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2023 suka bar Najeriya zuwa Landan a kasar Birtaniya.

Asiwaju Bola Tinubu da Sanata Kashim Shettima sun zabi su samu hutu ne domin su shiryawa yakin neman zaben shugabancin Najeriya da kyau.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Za Ta Fara Yakin Neman Zabe da Addu’o’in Musamman na Neman Sa’a

Kamar yadda hukumar INEC mai gudanar da zabe ta kasa ta shirya, nan da kwanaki biyu za a bude kofar fara yakin kujerar shugaban kasa na 2023.

Tinubu ya je hutu - Kwamitin kamfe

Jaridar tace Darektan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Bola Tinubu, Bayo Onanuga, ya tabbatar da wannan labari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayo Onanuga yace mai gidansa ya dauki hutun mako guda ne domin ya sarara. Premium Times ta fitar da makamancin wannan rahoto dazu.

Onanuga yace sai ranar 8 ga watan Oktoba ne Tinubu zai soma kamfe a Najeriya. Kafin nan za a shiga addu’o’i wajen yi wa APC samun nasara.

Magoya baya za su shiga tattaki

Ana haka ne kuma sai Pulse ta rahoto cewa magoya bayan Bola Tinubu za su fara tattakin mutane miliyan daya domin nuna karfin da suke da shi.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Tsohon Sakataren Buhari Ya Fallasa Wasu Kulle-Kullen da Tinubu Ke Yi Gabanin 2023

Shehu La’Shek Yahaya ya fitar da jawabi cewa kungiyoyin City Boy Movement da National Coalition Group za su shirya gangamin a birnin Abuja.

Tinubu
Bola Tinubu a filin jirgi kwanaki Hoto: punchng.com
Asali: UGC

PDP sun fara shirin kamfe

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a lokacin da ake maganar Tinubu sun wuce Landan, shi ma Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya tafi kasar Birtaniyar.

Wike wanda ake rigima da shi a PDP, yana Landan tare da Gwamna Samuel Ortom na Benuwai.

Shi kuma Atiku Abubakar wanda yake rike da tutan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, ya dawo Najeriya bayan kwanaki a Turai.

Har ila yau, jigo a PDP, Bukola Saraki ya fada a Twitter cewa ya shigo Najeriya. Alamu na nuna shirin yakin neman zama shugaban kasan yana kankama.

Rikici zai kunno kai a APC

Ku na da labari, a halin yanzu, takarar shugaban kasar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu tana kasa, tana dabo a tafiyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi Da Musulmi: Jerin Mukaman Da Kiristocin Najeriya Za Su Iya Samu A Gwamnatin Tinubu

Kungiyar gwamnoni na Progressive Governors’ Forum (PGF), suna zargin an yi watsi da mutanen da suka ce a sa a aikin kamfe na Tinubu a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel