Jam’iyyar APC Za Ta Fara Yakin Neman Zabe da Addu’o’in Musamman na Neman Sa’a

Jam’iyyar APC Za Ta Fara Yakin Neman Zabe da Addu’o’in Musamman na Neman Sa’a

  • Kwamitin yakin neman zaben Asiwaju Bola Tinubu ya fitar da yadda za a soma gudanar da kamfe
  • Darektan yada labarai da hulda da jama’a yace za a shirya addu’o’i na musamman a makon nan
  • Bayan addu’o’in, magoya baya zasu yi tattaki domin nuna goyon baya ga Tinubu/Shettima

Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki za ta fara yakin neman zaben shugaban kasa ne da addu’o’i na musamman da wani kewaye da za tayi a garin Abuja.

Bayo Onanuga ya fitar da jawabi a ranar Litinin, yana bayanin yadda shirin neman takarar Bola Tinubu zai kasance, Tribune ta kawo wannan rahoton.

Darektan yada labarai da hulda da jama’a na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Onanuga yace za a gudanar da addu'o'i a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Kwamitin kamfe Ya Yi Martani ga Gwamnonin APC da Suka yi Fushi da Bola Tinubu

A cewar kakakin kwamitin na kamfe, bayan addu’o’in da za ayi, za a mika takardun shiga kwamitin takaran APC ga wadanda aka ba aikin kamfen.

Jawabin Bayo Onanuga

“A madadin shugaban kwamitin yakin neman zabe, shugaba Muhammadu Buhari, ‘dan takararmu Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da abokin tafiyarsa, Kashim Shettima, muna taya ‘yan kwamitin takara murna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Bayo Onanuga

Daily Trust ta rahoto Onanuga yana cewa samun kujera a kwamitin kamfe damar bautawa jam’iyya ne wanda ke bukatar jajircewa da hidimtawa.

Asiwaju Tinubu
Kwamitin yakin neman zaben Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

PCC: 'Yan kwamiti sai sun yi da gaske

"Kwamitin neman zabe yana sa ran duka ‘yan kwamitin za su yi aiki sosai wajen ganin jam’iyyarmu ta APC ta samu nasara a zaben shugaban Najeriya na 2023.”
“Za a yi tatattakin lumuna da zarar an gama addu’o’in. A ranar za a ba wadanda aka zaba takarda.”

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sake Barin Najeriya, Masoyan ‘Dan Takara Sun Fito da Shirin da Suke yi

“Jam’iyya da ‘yan takara sun yaba da kokarinku da irin dukiya da karfi da kuka bada wajen wannan aiki tun da aka fara wannan tafiya, muna rokon ku cigaba."
“PCC za iyi aiki da kungiyoyin magoya-baya yayin da muke shiryawa kakar yakin neman zabe."

- Bayo Onanuga

A karshe, Vanguard ta rahoto Onanuga yana kira ga kungiyoyin da ke tallata APC a zaben 2023, suyi rajista da kwamitin PCC domin a ji dadin yin aiki tare.

Tinubu yana ina?

A yau aka samu rahoto Bola Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima sun lula Landan, ‘Yan takaran sun yi tafiya ne ana daf da soma kamfen 2023.

Bayo Onanuga ya fadi lokacin da ‘dan takaran na All Progressives Congress zai dawo gida. Da alama dai za a fara yakin kamfe ne shi Tinubu yana ketare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel