Majalisar Dattawa Ka Iya Sauya Tunani Kan Dakatar da Sanata Abdul Ningi

Majalisar Dattawa Ka Iya Sauya Tunani Kan Dakatar da Sanata Abdul Ningi

  • Majalisar dattawa ta fara duba yiwuwar sake tattauna batun dakatar da Sanata Abdul Ningi, mamba mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta Tsakiya
  • Mai magana da yawun majalisar ya bayyana cewa sanatocin da suka amince da dakatar da Ningi, suke da ikon dawo da shi bakin aiki
  • Tun farko an dakatar da sanatan ne bayan ya yi zargin cewa an yi cushen N3.7trn a kasafin kuɗin 2024

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar dattawa ta bayyana cewa da yiwuwar ta sake duba matakin da ta ɗauka na dakatar da Sanata Abdul Ningi mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta Tsakiya.

An dakatar da Ningi na tsawon watanni uku saboda ikirarin da ya yi a wata hira da sashen Hausa na BBC cewa majalisar tarayya ta yi cushe a kasafin kudin 2024.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya nemi hadin kan kasashe kan matsalar da ta addabi duniya

Majalisar dattawa.
Da yiwuwar sanatoci su sake nazari kan dakatar Sanata Abdul Ningi Hoto: NGRSenate
Asali: Twitter

Sanatan, wanda Femi Falana SAN ke goyon baya, ya ba shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, mako ɗaya ya soke dakatar da shi ko su fara shari'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake mayar da martani, Akpabio ya ce ba da son zuciyarsa ya dakatar da Ningi ba, mataki ne da sanatoci 108 cikin 109 suka amince da shi, Daily Trust ta ruwaito.

Majalisa za ta sake duba lamarin Ningi

Da yake magana yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin, kakakin majalisar dattawa, Yemi Adaramodu, ya ce za a duba batun Ningi.

A cewarsa, majalisar dattawa za ta sake duba batun dakatar da Ningi bayan sanatoci sun dawo daga hutu ranar Talata.

Sanata Adaramodu ya jaddada cewa duk wani hukunci na dawo da Ningi zai buƙaci kowane mamban majalisar dattawa, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Tsohon shugaban APC ya dauki zafi kan dambarwar, ya soki gwamna mai ci

Ya kuma yi bayanin cewa ba Akpabio ya dauki matakin dakatar da Ningi shi kaɗai ba, sai dai mataki ne da sanatoci 108 suka ɗauka har da Ningi da kansa.

“Sanatoci 108 har da Sanata Ningi sun yanke shawarar cewa za a yi wa Sanatan hukunci mai sauki na dakatar da shi na tsawon watanni uku daga ayyukan majalisa.
"Saboda haka waɗannan sanatoci 108 da suka ɗauki wannan mataki sune za su iya kiran Sanata Ningi ya dawo cikin majalisa.
"Muna hutu kusan makonni hudu kenan. Don haka idan muka koma gobe (Talata), shi abokin aikinmu ne, idan ya ba da haƙuri, to ‘yan majalisar dattawa za su duba, mu yi abin da ya dace."

- Yemi Adaramodu

Ningi: Atiku ya gana da 'Dan majalisa

A wani rahoton kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar tare da Dino Melaye sun ziyarci dakataccen sanatan Bauchi ta Tsakiya.

A bidiyon da ya bayyana, an ga Melaye yana shaguɓe ga majalisar dattawan Najeriya kan dakatar da Sanata Abdul Ningi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel