Tikitin Musulmi Da Musulmi: Jerin Mukaman Da Kiristocin Najeriya Za Su Iya Samu A Gwamnatin Tinubu

Tikitin Musulmi Da Musulmi: Jerin Mukaman Da Kiristocin Najeriya Za Su Iya Samu A Gwamnatin Tinubu

  • Kungiyar matasan kirista na Tinubu/Shettima sun bayyana mukaman da za a iya bawa kiristoci a gwamnatin Tinubu
  • An bayyana hakan ne yayin sukar da ya biyo bayan zaben tsohon gwamnan na jihar Borno, Kashim Shettima, matsayin abokin takarar Tinubu
  • A cewar kungiyar matasan, ba dukkan abubuwan da yan siyasa ke fada bane kan tikitin musulmi da musulmi ne gaskiya

Bayan sukar da aka rika yi kan tikitin musulmi da musulmi da jam'iyyar APC ta yi, Kungiyar matasa kirista na 'Christian Youths Movement for Tinubu/Shettima' ta bayyana cewa akwai mukamai kiristoci za su iya samu idan Tinubu ya ci zaben 2023.

Bola Tinubu
Tikitin Musulmi Da Musulmi: Jerin Mukaman Da Aka Tanada Wa Kiristocin Najeriya A Gwamnatin Tinubu. Hoto: Bola Tinubu Support Group.
Asali: UGC

Idan za a iya tunawa zaben tsohon gwamnan na Jihar Borno, Kashim Shettim a matsayin abokin takarar Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023 ya janyo cece-kuce a kasar.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ba Zamu Koma Aji Ba, Kungiyar ASUU Ta Daukaka Kara

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar ta lissafa mukaman da za a iya bawa kiristoci kamar haka:

1. Shugaban Majalisar Tarayya

2. Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya

3. Sakataren Gwamnatin Tarayya

Jaridar The Punch ta rahoto cewa kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da shugabanta na kasa, Adeleke Emmanuel da Ogumah Segun suka rattabawa hannu.

Hakazalika, kungiyar matasan ta ce duk da ya ke wasu daga cikin maganganun da ake yi kan tikitin musulmi da musulmi gaskiya ne, wasu kawai maganganu marasa tushe ne daga wasu da ke tsoron ba za a dama da su a siyasan ba.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Yayin da wasu maganganun akwai gaskiya cikinsu, wasu kawai magiya ne na wadanda ke ganin ba za a dama da su ba a siyasa. Duk da cewa daidaiton addini na da muhimmanci, ya kamata su san abin da ya fi komai muhimmanci, mu zabi kawo cigaban Najeriya a yayin da duniya ke fama da kallubalen tattalin arziki, ba ra'ayin da ba zai afani al'umma ba.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Gana da Limaman Kiristoci, Yace Zabar Shettima ba Barazana bace Garesu

"Shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai na tarayya, SGF da wasu mukaman za su iya fada wa hannun kirista.
"Mu, a kungiyar Christian Youth Movement, muna kira ga yan Najeriya, na kowanne addini, su bari shugabanni masu kwarewa irin Tinubu da Shettima su jagoranci kasar mu zuwa tudun na tsira."

Ganduje Ya Bayyana Abin Da Mulkin Tinubu Za Ta Kawo Wa Najeriya

A wani rahoton, Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje da wasu manyan yan Najeriya sun ce gwamnatin Tinubu a 2023 zai gaggauta cigaba da bunkasa a kasar, rahoton The Nation.

Ganduje ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke amincewa da nadin da aka masa matsayin majibinci na kungiyar APC na hadin kan kasa (ANIM) a gidan gwamnatin Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel