Abin da ya sa Peter Obi Ya Lallaba Ya Bar PDP ba tare da Sanar da ko Atiku ba

Abin da ya sa Peter Obi Ya Lallaba Ya Bar PDP ba tare da Sanar da ko Atiku ba

  • Peter Obi bai fadawa kowa zai bar jam’iyyar PDP ba, sai kurum aka ga takardar murabus
  • ‘Dan siyasar ya fahimci Atiku Abubakar ba zai yi da shi ba a 2023, ya nemawa kansa mafita
  • Obi mai neman takaran shugaban kasa a LP ya bar PDP da ya fahimci ba zai tsira da tikiti ba

Abuja - Sababbin bayanai sun zo mana a game da dalilin Peter Obi na ficewa daga jam’iyyar hamayya ta PDP ba tare da ya sanar da kowa ba.

Kafin a ankara, sai aka ji tsohon ‘dan takarar mataimakin shugaban kasar ya sauya-sheka. Jaridar The Guardian ta kawo rahoto a game da lamarin.

Da aka yi hira da Atiku Abubakar kwanakin baya, ‘dan takarar shugaban kasar ya shaidawa Duniya cewa bai san da cewa Obi zai canza jam’iyya ba.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Fuskanci Matsala Tun Yanzu, Ana Hure Kunnen Darektan Kamfen da Ya Zaba

Duk da shi ya fara ba shi damar takara a babban zabe, Atiku Abubakar yace tsohon Gwamnan jihar Anambra bai fada masa zai fita daga PDP ba.

Peter Obi bai ga haske a PDP ba

Binciken da jaridar tayi, ya nuna cewa ‘dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar LP ya dauki wannan mataki ne bayan lura da yanayin siyasar PDP.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Alamu sun nuna zai yi wahala jam’iyyar PDP ta tsaida Peter Obi a matsayin ‘dan takaran 2023.

Peter Obi
Peter Obi da Atiku Abubakar Hoto: wuzupnigeria.ng
Asali: UGC

Peter Obi ya fahimci Atiku Abubakar bai da nufin dauko abokin takararsa daga yankin Kudu maso gabas – bangaren da Obi ya fito (jihar Anambra).

Tun farko da Atiku ya zabi Obi ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasana zaben 2019, hakan ya jawo sabani tsakaninsa da gwamnonin yankin.

Atiku bai lissafi da Obi a 2023

Kara karanta wannan

Jigon PDP: Muna nan daku, El-Rufai zai lallaba ya koma jam'iyyar PDP nan da 2023

Wani na-kusa da Peter Obi ya shaidawa Guardian cewa Atiku ya nuna sha’awar daya daga cikin wadanda suka yi takara a kananan jam’iyyu a zaben 2019.

Duk da ba su je ko ina, Atiku ya fara hangen irinsu Kingsley Moghalu, har alamu sun fara nuna zai iya tafiya da su, hakan ya sa Obi ya kama hanyarsa.

Daf da karshen watan Yuni ne tsohon ‘dan takaran ya bada sanarwar barin PDP, sai ya wuce Landan, yana dawowa gida, ya bada sanarwar komawa LP.

Ba kowa za mu zaba ba - Wike

Dazu aka samu rahoto cewa rikicin PDP na neman komawa danye, inda sulhu tsakanin Atiku Abubakar da su Nyesom Wike ya jagwalgwale a makon nan.

Gwamna Wike ya tunawa Atiku Abubakar da Shugabannin PDP cewa babu wanda ya isa ya ci zabe a Ribas, yace shi ne yake rike da madafan iko a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel