2023: Masu assasa tikitin Musulmi da Musulmi basu yi wa Najeriya fatan alheri, Sheikh Maraya

2023: Masu assasa tikitin Musulmi da Musulmi basu yi wa Najeriya fatan alheri, Sheikh Maraya

  • Tsohon hadimin gwamnan jihar Kaduna kan lamurran da suka shafi addinin musuluncin da aikin Hajji, Sheikh Haliru Abdullahi Maraya ya ce goyon bayan bada tikiti takara daga addini guda ba adalci bane
  • A cewar fitaccen malamin addinin musuluncin, babu musulmin da zai taba amincewa da tikitin Kirista da Kirista a siyasar Najeriya ballantana a halin da ake ciki a yanzu
  • Haka zalika, addinin musulunci ya yi umarni da yin adalci ga kowa ba tare da dubi da addini, kabila ko yare ba, mafitar ita ce tikitin musulmi da kirista don cigaba da tabbatar da zaman lafiya

Tsohon hadimin gwamnan jihar Kaduna a lamurran da suka shafi Musulunci da Hajji, Sheikh Haliru Abdullahi Maraya ya ce wadanda suke assasa dabarar tikitin Musulmi da Musulmi ko Kirista da Kirista a yau a Najeriya, basa wa kasar fatan alkhairi, musamman yanzu da Najeriya ta rabu gida biyu tare da matsalolin addini.

Kara karanta wannan

PDP ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tuhumi Buratai kan kudin makamai

Masu saka kuri'a
2023: Masu assasa tikitin Musulmi da Musulmi basu yi wa Najeriya fatan alheri, Sheikh Maraya
Asali: UGC

"Ina mamakin yadda kasar za ta koma da tarin matsalolin addini. Babu addinin da yake da karfin tsaida 'dan takarar da mataimakinsa idan har cancanta shi ne abun dubawa wajen zaben abokan tafiya," a cewarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata takarda mai taken 'Ra'ayin musulunci game da tikitin tsayawa takarar shugaban kasa duk daga addini daya,' Sheikh Maraya ya ce "bana tunanin akwai musulmin da zai amince da tikitin takarar shugaban kasar Kirista da Kirista. Babu shakka, musulmai za su koka a kan janyo rashin adalcin da aka nuna musu."
A cewar fitaccen malamin addinin musuluncin," Najeriya kasa ce da ke da addinai daban-daban wacce ke da sama da musulmai 200 miliyan. Haka zalika, mutum zai iya cewa akwai sama da 200 miliyan daga addinai daban-daban. Dan a yi adalci ga dukkan 'yan kasa, tare da kawo daidaito tsakanin addinai a kasar, 'yan siyasan Najeriya da manyan jam'iyyun siyasa sun guji tsaida 'yan takara daga addini daya tun siyasar 1999."

Kara karanta wannan

Duk daya muke: Kristoci sun taya musulmai cire ciyayi a masalacin Kaduna.

"Hada tikitin takarar shugaban kasar musulmi da wanda ba musulmi ba a Najeriya a yau, ya bada wata kafar yin adalci, kawo daidaito kamar yadda addinin musulunci ya koyar.

Vanguard ta ruwaito cewa, yace addinin musulunci yana umarni da yin adalci ga kowa ba tare da wani bambanci ba, na addini ne, kabila, yanki, yare, bambancin tsakanin mutane.

Kur'ani na cewa: "Sannan kada ku bari kiyayyar mutane su kangeku daga yi musu adalci" (Q5:8). Saboda haka ba daidai bane musulmi ya goyi bayan tikitin Musulmi da Musulmi, domin hakan ya karo da adalcin da muslunci ke goyon baya tare da dagaro da hakan a koda yaushe."
"Allah (SWT) ya haramta duk wani irin rashin adalci ga kansa, kuma ya haramta tsakanin bayinsa. Saboda haka, 'yan siyasarmu a koda yaushe su yi kokarin ganin sun kare hadin kan kasarmu, Najeriya. Ga jam'iyyar siyasa ta dora musulmai a matsayin shugaban jam'iyya, 'dan takarar shugaban kasa da mataimaki, wannan jam'iyyar bata a matakin da zata ce tana kwatanta adalci," a cewarsa.

Kara karanta wannan

Duk Daya ne: Kiristoci sun taya Musulmai share Masallacin Sallar Idi a Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel