Da Duminsa: Ɗan majalisar wakilai ya bi sahun Sanatocin APC uku, ya fice daga jam'iyyar

Da Duminsa: Ɗan majalisar wakilai ya bi sahun Sanatocin APC uku, ya fice daga jam'iyyar

  • Jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan ta shiga ruɗani yayin da yan majalisun tarayya ke ta fice wa a yau Talata
  • Bayan Sanatoci uku a majalisar Dattawa, wani mamba a majalisar wakilai ya sanar da ficewarsa a hukumance
  • Honorabul Shina Peller, ya ce bayan tattaunawa da jam'iyyun siyasa ya zaɓi ya koma jam'iyyar Accord Party

Oyo - Ɗan majalisar wakilan tarayya daga jihar Oyo, Shina Peller, ya fice daga jam'iyyar All Progressive Congress wato APC a hukumance, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Honorabul Peller, wanda ya sanar da murabus ɗinsa a zauren majalisar wakilan tarayya yayin zaman yau Talata, ya ce ya koma jam'iyyar Accord Party.

Shina Peller.
Da Duminsa: Ɗan majalisar wakilai ya bi sahun Sanatocin APC uku, ya fice daga jam'iyyar Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kafin sauya shekarsa, ɗan majalisar ya sha kaye a zaɓen fidda ɗan takarar Sanatan jihar Oyo ta arewa a hannun Fatai Buhari, wanda ya fito daga yankin Ogbomoso.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Majalisar dattawa ta nada sabon shugaban marasa rinjaye

Wasu masu sharhi kan harkokokin siyasa sun yi imani cewa ficewarsa daga APC na da alaƙa da rashin nasarar da ya yi a zaɓen fidda gwani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Meyasa ya zaɓi ya koma Accord Party?

Mista Peller ya ce:

"Bayan na bar APC, muka fara tattaunawa da wasu jam'iyyu, muna da zaɓi da dama a gaban mu amma muka zaɓi Accord Party saboda wasu dalilai. Jam'iyyar AP ita ce ta farko da ta yanke kai tikitin Sanatan Oyo ta arewa yankin Oke Ogun."
"Jam'iyyar ta nuna tana kaunar mutanen Oke Ogun, kuma ta hura wa fatan su rai, kuma su san cewa ana yi da su. Accord Party tana da tsari mai kyau a cikin gida ba kamar sauran jam'iyyu ba."
"A yau, ina mai sanar wa al'umma cewa na koma jam'iyyar AP, kuma a koda yaushe tambarin Accord na tuna mun wasu yan Najeriya masu muhimmanci da suka yi wa al'umma aiki."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mai Gari Da Dansa Da Aka Sace a Bauchi Sun Shaki Iskar Yanci Bayan Kwana 3 Hannun Yan Bindiga

Mista Peller, yanzu haka shi ne ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Iseyin/Itesiwaju/Kajola/Iwajowa a majalisar wakilan tarayya.

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar babban jigon APC ɗan takara a 2023

Myagun yan bindiga sun kutsa har cikin gida sun sace mahaifiyar ɗan takarar Sanatan Jigawa ta tsakiya a garin Kiyawa.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Shisu, ya ce tuni kwamishina ya haɗa tawagar dakaru na musamman don ceto matar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel