Gwamna Okowa ya yi magana kan dalilin daukarsa da Atiku ya yi a maimakon ya zabi Wike

Gwamna Okowa ya yi magana kan dalilin daukarsa da Atiku ya yi a maimakon ya zabi Wike

  • Dr. Ifeanyi Okowa ya ce Nyesom Wike ba zai ji wani haushi saboda Atiku Abubakar bai dauke shi ba
  • Okowa wanda aka zaba ya ce a sunnar siyasa, ba zai yiwu mutum biyu su samu mukami daya ba
  • Gwamnan ya na ganin Wike ba zai yi fushi saboda bai samu takarar mataimakin shugaban kasa ba

Abuja - Dr. Ifeanyi Okowa ya fito yana bayani a game da zaben sa da Atiku Abubakar ya yi a matsayin abokin takararsa a zabe mai zuwa na 2023.

Ifeanyi Okowa wanda shi ne Gwamnan jihar Delta a halin yanzu, ya ce Gwamna Nyesom Wike ba zai ji haushi saboda ya zama abokin takara a PDP ba.

Jaridar Daily Trust a rahoton da ta fitar a ranar Alhamis, ta ce Okowa ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Bayan tantance shi a matsayin ‘dan takarar matamakin shugaban kasa, Okowa ya shaidawa ‘yan jarida cewa Wike yana da kishin kasa da son jam’iyya.

Gwamna Okowa ya kara da cewa abokin aikin na sa ya san mutum daya rak za a iya dauka.

Okowa
Sanata Okowa a Sakatariyar PDP Hoto: @IAOkowa
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wike 'dan a-mutun PDP

“Gwamna Wike rikakken ‘dan jam’iyya ne wanda yake matukar kaunar jam’iyyarmu, kuma na yi imani ya yarda da tsarin damukaradiyya.”
“Ya fahimci idan ‘yanuwa da yawa su na harin kujera, dole mutum daya zai iya samu lokaci guda.
“Ina son in tabbatar maku da cewa Gwamna Wike mutumin kirki ne wanda kaunar kasar nan da jam’iyyar nan zai sa ya shawo kan duk kalubale.”
“Mutum ne mai karfin hali, kuma ba na tunanin ran shi zai baci.” – Ifeanyi Okowa.

Mutanen Wike sun kauracewa Sakatariya

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Dakatar Yakin Neman Zabe Kan Abu Ɗaya Da Ya Shafi Yan Najeriya

Jaridar ta ce Okowa ya ce mutane su fara shiri domin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar zai shiga kamfe gadan-gadan domin lashe zabe.

An fahimci gwamnonin da suke tare da Wike ba su halarci wannan taro ba. Amma an ga tsohon Gwamnan Delta, Ifeanyi Ugwuanyi a sakatariyar jam’iyyar.

Gwamna Bala Mohammed, Udom Emmanuel, Douye Diri da Godwin Obaseki sun halarci taron.

Ya aka yi haka?

Ku na da labari babu mamaki daga cikin abin da ya sa Ifeanyi Okowa ya yi wa Nyesom Wike kafa akwai sarkakiyar da ke cikin sabuwar dokar zabe na kasa.

Nyesom Wike ya yaki Atiku Abubakar Abubakar ido-rufe wajen neman takara a PDP, shi kuwa Sanata Okowa ya taimakawa Atiku wajen samun nasara ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel