Yobe: Fusatattun Mambobin APC Zasu Maka Jam'iyya a Kotu Kan Zaben Fidda Gwani

Yobe: Fusatattun Mambobin APC Zasu Maka Jam'iyya a Kotu Kan Zaben Fidda Gwani

  • Wasu fusatattun mabobin jam'iyyar APC a jihar Yobe suna barazanar maka jam'iyyar a kotu kan zaben fidda gwani
  • A cewarsu, kujerun majalisar tarayya 2 da na majalisar jiha 5 ne aka ki yin zabukan, aka kakaba musu 'yan takarar son rai
  • Shugaban Kungiyar, Musa Yusuf, ya ce sun yi duk abinda ya dace na mika korafi amma shugaban jam'iyyar na jihar ya ki daukan mataki

Yobe - Wata kungiyar fusatattun 'yan takara a jam'iyyar APC a zaben fidda gwani na jam'iyyar da aka yi a jihar Yobe suna barazanar maka jam'iyyar a kotu idan ta gaza shawo kan matsalolinsu.

Mai magana da yawun kungiyar, Musa Yusuf, ya sanar da Premium Times cewa kungiyar ta karar da duka wani kokarinta na shawo kan matsalar a cikin gida tunda shugaban jam'iyyar na jihar ya yi kunnen uwar shegu da su.

Kara karanta wannan

2023: Hadimin Ganduje Ya Bayyana Dalilan da Suka sa Ya Dace Ya Zama Mataimakin Tinubu

Logon jam'iyyar All Progressive Congress
Yobe: Fusatattun Mambobin APC Zasu Maka Jam'iyya a Kotu Kan Zaben Fidda Gwani. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yusuf ya bayyana cewa ba a yi zabe a mazabu biyu na tarayya ba a jihar kuma ba a yi a mazabu biyar na majalisar jihar ba.

"Ba za mu kalmashe hannu mu bar hakkin mutane ya wuce muna kallo ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Za mu sha mamaki idan aka ce muku duk wuraren da ba a yi zaben ba an saka 'yan takara da ake so," yace.
"Abinda muka yanke hukuncin a matsayin mu na kungiya shi ne mu je kotu don bin kadin jama'a. Ba za mu fara tashin-tashina ba. A maimakon hakan, mun rike wuta tare da shawo kan magoya bayanmu kan cewa kada su fara tada hankula.
"Za mu tafi kotu domin sauke fushinmu. Mun yarda cewa idan jam'iyya ba za ta saurare mu ba, kotu ce za ta fitar mana da hakkinmu. Muna bibiyar abun nan ne ba don kanmu ba, sai saboda son kai da aka nuna mana."

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

Yusuf ya lissafo mazabu da 'yan takarar da lamarin ya shafa:

1. Potiskum ta tsakiya a majalisar jiha Barista Mohammed Khalil da Hon. Ahmed Adamu

2. Mazabar Fika/Ngalda ta jiha Yakubu Sulaiman da Musa A. Yusuf

3. Bade/Jakusko a matakin tarayya Zakari Yau Galadima da Sani Ahmed Kaitafi

4. Nangere/ Potiskum a matakin tarayya. Fatsuma Talba da Hon Mohammed Adamu

5. Fika/Fune a matakin tarayya Aliyu Mohammed SK da Barista Idriss Abubakar Yarima Ajeje

6. Goya/Ngeji a matakin jiha Ishaku Sani Audu da Abdulmumini Hussaini

7. Nangere a matakin jiha Saminu Musa Lawan da Abdulhamid Degubi

Kungiyar ta yi kira ga gwamna Mai Mala Buni na jihar da NWC na APC da su shiga lamarin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng