Rikicin gida ya jawowa APC rashi, INEC ba ta san da zaman ‘Dan takarar Gwamnanta ba

Rikicin gida ya jawowa APC rashi, INEC ba ta san da zaman ‘Dan takarar Gwamnanta ba

  • Hukumar INEC ta tabbatar da cewa APC ba ta da wani ‘dan takarar kujerar Gwamna a Akwa Ibom
  • Jam’iyyar APC ta tsunduma cikin rikici, Godswill Akpabio yana goyon bayan ‘yan taware a jihar
  • Hakan ya jawo har lokaci ya kure ba tare da APC ta iya gudanar da zaben ‘dan takarar gwamna ba

Akwa Ibom - A jihar Akwa Ibom, hukumar zabe na kasa watau INEC ta ce jam’iyyar APC ba ta da ‘dan takarar kujerar gwamna a zaben 2023 da za ayi.

The Nation ta ce an samu wannan labari ne daga wani rahoto da Babban Kwamishinan hukumar INEC na Akwa Ibom, Mike Igini ya aika zuwa hedikwata.

Mike Igini ya sanar da hukumar zabe na kasa cewa jam’iyyar APC ba ta iya gudanar da zaben tsaida ‘dan takarar gwamna a ranar 26 ga watan Mayu ba.

Kara karanta wannan

Barazana da kalubale 8 da Bola Tinubu ya fuskanta wajen zama ‘Dan takaran APC a 2023

Igini wanda shi ne Jami’in REC a jihar, ya ce zaben ‘dan takaran Gwamna da aka shirya za ayi a wani wurin taro a garin Uyo a ranar da aka tsaida bai yiwu ba.

Zaben tsaida gwani bai yiwu ba

Kwamishinan zaben yake cewa ya ziyarci Sheergrace Arena tare da Kwamishinan ‘yan sanda na Akwa Ibom, Andrew Amiengheme, amma ba su iske kowa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga baya labari ya zo cewa wasu fusatattun ‘ya ‘yan jam’iyyar APC ne suka tsare ‘yan kwamitin da za su gudanar da zaben fito da ‘dan takaran na zaben 2023.

‘Dan takarar Gwamnan Akwa Ibom
John Akpanudoedehe ya koma NNPP Hoto: SaifullahiHon
Asali: Twitter

Rahoton ya ce hakan ta sa aka tura jami’an DSS domin ceto mutanen da aka tsare a hanyar Uyo.

Ko da aka ceto wadannan mutane, shugaban kwamitin APC na shirya zaben tsaida gwani a Akwa Ibom, Tunde Ajibulu, bai iya gudanar da zaben a lokacin ba.

Kara karanta wannan

Zaben APC: Yadda Gwamnoni, Jagororin Arewa da ‘Yan NWC suka ba Bola Tinubu nasara

Premium Times ta ce wannan rahoto da ya je gaban INEC, ya yi daidai da labarin da ta fitar kwanaki, ta nuna APC ba ta zabi ‘dan takarar Gwamnanta ba.

Ana rigima a reshen jam’iyyar na jihar Akwa Ibom ne a dalilin goyon bayan ‘yan taware da Sanata Godswill Akpabio yake yi, har suka tsaida Akan Udofia a APC.

Abokan fadan Akpabio su na cewa 'dan takarar gwamnansa, Udofia bai wuce waya daya a APC ba.

John Akpanudoedehe ya bar APC

Rahoton da mu ka fitar kwanaki ya nuna tsohon sakataren APC na riko na kasa, Sanata John James Akpanudoedehe, ya fice daga jam'iyya mai mulkin kasa.

Wani daga cikin magoya bayan APC ya zargi John Akpanudoedehe da haddasa rigimar cikin gidan PDP saboda burinsa, a karshe ya koma jam’iyyar kayan dadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng