Da dumi-dumi: Awanni kafin zaben fidda gwanin jam’iyyar, wani babban jigon APC ya sauya sheka

Da dumi-dumi: Awanni kafin zaben fidda gwanin jam’iyyar, wani babban jigon APC ya sauya sheka

  • Tsohon sakataren APC na riko na kasa, Sanata John James Akpanudoedehe, ya fice daga jam'iyyar mai mulki
  • Akpanudoedehe ya sanar da sauya shekar tasa ne a ranar Litinin, 6 ga watan Yuni, yan awanni kafin babban taron jam'iyyar
  • Dan siyasar ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin ne saboda tsarin da jam'iyyar ta bi wajen zabar yan takara a jiharsa ta Akwa Ibom

Akwa Ibom- Tsohon sakataren rusasshen kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata John James Akpanudoedehe ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar mai mulki.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Akpanudoedehe ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 6 ga watan Yuni, a cikin wata wasika zuwa ga shugaban APC na gudunmarsa, , Offot 6, a Uyo da ke jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Mataimakin gwamnan Oyo ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Da dumi-dumi: Awanni kafin zaben fidda gwanin jam’iyyar, wani babban jigon APC ya sauya sheka
Da dumi-dumi: Awanni kafin zaben fidda gwanin jam’iyyar, wani babban jigon APC ya sauya sheka Hoto: naijanews.com
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta nakalto wasikar na cewa:

“Na rubuta wannan takarda don sanar da kai batun ficewata daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), nan take.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Daga yanzu, ni ba dan APC bane a unguwata (gudunma ta 6 a karamar hukumar Uyo) ko kuma a ko’ina. Saboda haka na sauke dukkanin hakokin da ya rataya a wuyana a matsayina na dan APC, mamba na kwamitin shawarwari da kuma mamba na kwamitin masu ruwa da tsaki na APC na kasa.
“Wannan hukunci nawa na raba hanya da APC mai tsauri ne, amma shugabanci ya kunshi bin ra’ayin makusanta, abokan tarayya mafi rinjaye, da magoya bayan da suka nuna rikon amana na tsawon lokaci, kuma a yanzu sun shaida yadda jam’iyyar APC ta bijire wajen tafiyar da tsarin zabar 'yan takara a jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: APC ta magantu kan batun takarar Jonathan a zaben fidda gwanin shugaban kasa

“Babban burinmu na yiwa mutanen jiharmu mai albarka hidima yana nan a kan gaba.”

Da dumi-dumi: Adamu ya bayyana Lawan a matsayin dan takarar maslaha

A wani labarin, mun ji cewa rikici ya barke a jam’iyyar APC biyo bayan sanarwar da shugaban APC Adamu ya sanar da shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa da kwamiti ya amince dashi, Sanata Abdullahi Adamu ya yi.

Adamu ya bayyana hakan ne a taron kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na APC ranar Litinin a Abuja.

Sauran ‘yan takarar da suka hada da Asiwaju Bola Tinubu; Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Dokta Kayode Fayemi da David Umahi, da dai sauransu za a ba su damar gwabza zaben fidda gwani a taron da za a yi gobe a dandalin Eagle Square, Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel