Zaɓen Magajin Buhari: Yan jaridu sun yi cirko-cirko a kofar shiga Filin taron APC kan abu ɗaya

Zaɓen Magajin Buhari: Yan jaridu sun yi cirko-cirko a kofar shiga Filin taron APC kan abu ɗaya

  • A rana ta biyu na babban taron APC na zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa, ayyuka sun kankama kuma shirye-shirye sun yi nisa
  • Sai dai har yanzun yan jaridun da suka je ɗakko abun da ke wakana ba su samu damar shiga ba sanadiyyar gazawar APC
  • Kwamitin midiya karkashin shugabancin gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya gaza ba su katin shaidar aiki wato 'Tags'

Abuja - Yan jaridun da aka tura domin su ɗakko abubuwan da ke faruwa a babban taron APC na ƙasa da ke gudana a Filin Eagle Square Abuja sun gaza samun damar shiga.

Daily Trust ta tattaro cewa hakan ta faru ne bisa gazawar kwamitin jam'iyyar APC na ɓangaren midiya karkashin gwamna Abdullahi Sule. Har yanzu kwamitin bai raba wa yan jaridun katin shaida ba 'Tags'.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin APC: 'Yan takara na ta bin deliget har otal domin neman hadin kai

An hana yan jaridu shiga.
Zaɓen Magajin Buhari: Yan jaridu sun yi cirko-cirko a kofar shiga Filin taron APC kan abu ɗaya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A wata sanarwa da jam'iyyar APC ta fitar dangane da taron, za'a fara aiwatar da abun da ya tara mutane wurin da misalin ƙarfe 10:00 na safe, farawa da isowar Deleget.

Tun mako biyu kafin wannan rana, Gidajen jaridu waɗanda suka shirya ma'aikatan da zasu ɗakko musu rahoton abin da ke faruwa, sun rubuta takardan neman izinin APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun ƙara da bayyana cewa hatta masu tattara rahotannin jam'iyyar APC na babbar Sakatariya ta Abuja na nan na jiran a ba su nasu katunan don shiga wurin.

Yan jaridun da suka isa Filin Eagle Square tun da sanyin safiyar Talata, suna nan zaune suna cigaba da jiran sahalewar jam'iyya domin jami'an tsaron da aka girke a wurin sun hana su shiga.

A wani labarin kuma Wani ma'aikacin gwamnati ya maka Jaruma Hadiza Gabon a Kotu sabida taƙi aurensa bayan ta lakume masa kuɗi

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC sun tattauna da NWC, Adamu bai samu halarta ba

Wani ma'aikaci ya kai karar jaruma Hadiza Gabon gaban Kotun Shari'ar Musulunci kan ta karya masa alƙawarin aure.

Bala Musa ya shaida wa Kotun sun jima suna soyayya da Gabon kuma ta masa alƙawarin aure, shiyasa da ta nemi Kuɗi yake tura mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel