Gwamnonin APC sun tattauna da NWC, Adamu bai samu halarta ba

Gwamnonin APC sun tattauna da NWC, Adamu bai samu halarta ba

  • Gwamnonin jam'iyya mai mulki ta APC na arewacin Najeriya sun gana da juna a Abuja, sai da Abdullahi Adamu bai samu halarta ba
  • Bayan kammala taron, gwamnonin sun ce ya zama dole su karasa gidan Abdullahi Adamu da ke Abuja domin tattauna mafita
  • Duk da ba su bayyana makasudin taron ba, an san ba ya rasa nasaba da gagarumin taron zaben fidda gwani da za su yi

FCT, Abuja - Gwamnonin jam'iyyar APC sun gana da mambobin kwamitin ayyuka na kasa na jam'iyyar.

Sai dai, shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullahi Adamu, wanda ya dace ya kasance tare da su bai samu halarta ba, Premium Times ta ruwaito.

Gwamnonin APC sun tattauna da NWC, Adamu bai samu halarta ba
Gwamnonin APC sun tattauna da NWC, Adamu bai samu halarta ba. Hoto daga @OfficialAPCNg
Asali: UGC

A don haka, gwamnonin suka yanke hukuncin samun Adamu har gidansa domin tattauna kan gangamin zaben fitar da 'dan takara da za su yi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaban APC ya fusata, ya fatattaki 'yan jarida a sakateriyar APC

Wasu daga cikin gwamnonin sun hada da: Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, Atiku Bagudu na jihar Kebbi, Dapo Abiodun na jihar Ogun, Abdullahi Ganduje na jihar Kano da Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da ba a bayyana abubuwan da za a tattauna a taron ba, ba zai rasa alaka da bayyana Ahmad Lawan da Adamu yayi ba a matsayin dan takarar yarjejeniya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke so ba.

Shugaban jam'iyyar na kasa ya sanar da mambobin NWC a taron da suka yi cewa, Lawan shi ne 'dan takarar yarjejeniya da jam'iyyar ke so amma sauran 'yan takara za su iya cigaba da neman kujerar.

Tuni mambobin NWC suka yi watsi da wannan batun tare da alakanta hakan da ra'ayin Abdullahi Adamu.

A yayin jawabi ga manema labarai bayan taro da gwamnonin, mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa daga arewa, Abubakar Kyari, ya ce har yanzu jam'iyyar ba ta fitar da 'dan takarar yarjejeniya ba.

Kara karanta wannan

Maslaha: An bayyana shugaban majalisa Lawan a matsayin dan takarar APC

Ya ce za su cigaba da taron a Abuja, gidan Adamu.

Tun farko, gwamnonin APC na arewacin Najeriya sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Aso Villa.

Bayan taron, gwamnonin sun jaddada cewa, a mika mulki ga yankin kudancin Najeriya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuwa ya tabbatar musu da cewa babu 'dan takarar da ya ke goyon baya.

Kowa ya bi: An sake samun Gwamnan Arewa da ke goyon bayan ‘Yan kudu su karbe mulki

A wani labari na daban, Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq na jihar Kwara ya ce yana goyon bayan matsayar shugabannin Arewa na cewa a kai mulki kudu a 2023.

Mai girma Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq ya bayyana haka ne a lokacin da yake maidawa jaridar Daily Trust ganin cewa ba a ga sa hannunsa ba.

Abdulrahman AbdulRazaq bai cikin gwamnonin APC na shiyyar Arewacin Najeriya da suka hadu a kan a fito da ‘dan takarar shugaban kasa daga kudu.

Kara karanta wannan

Jajiberin Zaben Fidda Gwani: Buhari Ya Ci Abincin Dare Tare da Adamu da Gwamnoni

Asali: Legit.ng

Online view pixel