Jam’iyyar NNPP ta dura zauren Majalisar Dattawa, Sanatan Bauchi ya yi watsi da APC

Jam’iyyar NNPP ta dura zauren Majalisar Dattawa, Sanatan Bauchi ya yi watsi da APC

Bisa dukkan alamu Lawan Yahaya Gumau ya tattara kayan shi, ya hakura da zama a jam’iyyar APC

An ga Sanata Lawan Yahaya Gumau dauke da fam na takarar ‘dan majalisar dattawa a jam’iyyar NNPP

Gumau yana cikin wadanda APC ta hana tikitin tazarce, amma bai cire ran komawa majalisa a 2023 ba

Bauchi - Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Sanata Lawan Yahaya Gumau ya fita daga jam’iyyar APC mai mulki, ya sauya-sheka ne zuwa NNPP.

Saifullahi Muhammad Hassan, daya daga cikin Hadiman jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso ne ya tabbatar da wannan labarin.

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa, Malam Saifullahi Hassan ya tabbatar da cewa Lawan Yahaya Gumau ya shiga jam’iyya mai kayan marmari.

Kara karanta wannan

Mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2023 zai iya zama Gwamnan da ya yi takara da shi

Bayan ya fice daga APC mai mulkin Najeriya da rinjaye a majalisar dattawa, Sanatan bai yi wata-wata ba, ya yanki fam a jam’iyyar hamayyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jawabin da Hassan ya fitar a ranar Laraba, 1 ga watan Yuni 2022, ya nuna Sanatan na kudancin Bauchi ya yanki fam din neman Sanata a NNPP.

APC ta hana Gumau takara

Sanata Gumau ya cin ma wannan mataki ne ganin cewa ya sha kasa a zaben tsaida ‘yan takarar Sanata da jam’iyyar APC ta shiya a jihar Bauchi.

Jam’iyyar NNPP ta kama Lawan Yahaya Gumau
Lawan Yahaya Gumau da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: SaifullahiMohHassan
Asali: Facebook

Gumau yana cikin ‘yan majalisa masu-ci da ba za su iya samun nasara a zaben tsaida gwani ba.

A hotunan da ke yawo, an ga Sanatan tare da Rabiu Kwankwaso da wasu mabiya darikar Kwankwasiyya rike da takardun shiga zabe a NNPP.

Gumau ya yi shekara 4 a Majalisa

Kara karanta wannan

NNPP ta shiga gidan tsohon Ministan Buhari, ‘Dan Majalisan Kano ya fice daga APC

‘Dan majalisar mai shekara 51 a Duniya ya zama Sanata ne a 2018, bayan rasuwar Sanata Isa Wakili, kafin na ‘dan majalisa ne na mazabar Toro.

Idan za a tuna Gumau ya samu gagarumar nasara a zaben cike gurbin da INEC ta gudanar, ya doke ‘dan takarar PDP a yankin kudancin jihar Bauchi.

Babu mamaki wasu daga cikin Sanatocin jihohin Arewa su dauki wannan salo, su sauya-sheka ganin jam’iyyunsu sun hana su damar zarcewa a ofis.

An yi bari a Bauchi

A rahoton da mu ka fitar, kun ji yadda duka Sanatoci uku da ke kan mulki su ka sha kasa a zaben fitar da gwanin jam’iyyar APC da aka shirya a Bauchi.

Muhammad Adamu Bulkachuwa ya yi mummunar faduwa a zaben, ya kare babu ko kuri'a daya. Shi ma Halliru Jika ya gagara samun takarar gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel